1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahajjata sun isa Muzdalifah bayan Arfa

Mouhamadou Awal Balarabe
July 30, 2020

A kasar saudiyyya, mahajatta sun kama hanyar zuwa Muzdalifah domin mutunta daya daga cikin rukunan aikin Hajji kamar yadda Islama ta tanada, bayan gudanar da hawan Arfa inda suka yi addu'o'i.

https://p.dw.com/p/3gCGh
Saudi-Arabien Mekka | Corona & Hadsch | Pilgerfahrt
Hoto: Reuters/Saudi Ministry of Media

Wannan zuwa Muzdalifah na zuwa ne bayan da mahajjata suka shafe yini guda na hawan Arfa da ke zama muhimmin ginshiki na aikin Hajji. Sai dai addu'o'in maniyatan sun gudana ne cikin tsauraran matakan tazara tsakaninsu tare da sanya takunkumi don kauce wa kamuwa da cutar corona. A kasar ta Saudiya dai mutane akalla dubu 272,590 ne suka  kamu da covid-19, ciki har da mutum 2,816 da cutar ta yi sanadiyyar mutuwarsu

A bana dai kasar Saudiyya ta haramta wa baki shigowa kasar don sauke farali sakamakon bullar cutar numfashi ta corona. Mutane dubu 10 da ke da zama a kasar mai tsarki ne kawai suka samu damar gudanar da bautar. Shi dai aikin hajji, yana daya daga cikin shika-shikan Musulunci da ake so kowanne Musulmi ya yi, ko da sau daya ne a rayuwa, idan dai yana da hali da kuma koshin lafiya.