Mahajjata na gudanar da tsayuwar Arfa
October 3, 2014Talla
Tun a jiya ne dai alhazan suka isa Muna kuma da sanyin safiyar Juma'ar nan ce suka dunguma zuwa dutsen Arfa don gudanar da aiyyukansu na ibada.
Hukumomin Saudiyya dai sun ce sun gudanar shirye-shirye a bana don kawar da duk wasu matsaloli da mahajjatan ka iya cin karo da su yayin da aikin hajjin na bana ya kai kololuwarsa.
Masu aiko da rahotanni dai na cewar komai na gudana lami lafiya ba tare da an fuskanci wani kalubale babba ba.