Magoya bayan Mursi na cikin fushi. | Siyasa | DW | 05.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Magoya bayan Mursi na cikin fushi.

Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi magoya bayan tsohon shugaban Masar sun lashi takobin ƙalubalantar gwamnatin.

Ba shakka waɗannan mutane suna cikin ɓacin rai kuma a shirye suke su fuskanci duk wani abinda ka iya zama cikas a garesu wajen cimma buƙatunsu. A kowane lungu na birnin Alƙahira za ka samu wani gungu na jama'ar 'Yan Uwa Musulumi da ke bi layi-layi suna faɗikar da al'umma da su fito ƙwansu da kwal-kwata domin bujere wa sojojin. To sai dai jama'ar na ƙoƙarin kaucewa yin amfani da wasu miyagun hanyoyin domin tayar da fitina a gangamin da suka ce na lumana ne.

Babu allamun ja da baya ga masu yin zanga-zangar.

slogans at the Raba El-Adwyia mosque square in Cairo July 4, 2013. The leader of the Muslim Brotherhood was arrested by Egyptian security forces on Thursday in a crackdown against the Islamist movement after the army ousted the country's first democratically elected president Mursi. At least 16 people have been killed and hundreds wounded in street clashes across Egypt since Mursi's overthrow. REUTERS/Louafi Larbi (EGYPT - Tags: POLITICS CIVIL UNREST MILITARY)--eingestellt von haz

Magoya bayan Mommed Mursi

Da dama dai daga cikin yan jam'iyyar ta 'Yan Uwa Musulumi ba su yi tsamanin ba haka zai faru ga Mohammed Mursi na faɗuwar gwamnatinsa ba shiri a cikin kwanaki fuɗu kwai na zanga-zangar ƙin jinin gwamnatinsa. Ko da shi ke har yanzu sojoji ba su aikata wani aikin asha ba, na fatattakar magoya bayan Mursi waɗanda suka yi cirko-cirko a cikin manyan titunan birnin Alƙahira. Amma ɗaya daga cikin magoya bayansa Mohammed Abdel Lam da ke a unguwar Nasir City da ke a tsakiyar Alƙahira ya ce an kai masu hari.

Inda ya ce a jiya wani sojin ya yi harbi a kan mutane guda uku ya ce kuma sojojin sun rufe gidajen talabijan na masu kishin addinin amma duk da haka ya ce ba za su yi fitina ba a zanga- zangar. Ya ce : ''za mu ci gaba da yin jerin gwano cikin lumuna domin nunawa duniya cewar Mursi sh ne ke da rinjaye na jama'a.''

Nuna damuwar jama'ar ƙasar dangane da halin da ake ciki.

A protester, who supports former Egyptian President Mohamed Mursi, chants slogans during a rally near Cairo University after Friday prayers in Cairo July 5, 2013. Islamist allies of ousted president Mursi called on people to protest on Friday to express outrage at his overthrow by the army and to reject a planned interim government backed by their liberal opponents. REUTERS/Suhaib Salem (EGYPT - Tags: POLITICS CIVIL UNREST TPX IMAGES OF THE DAY)

Magoya bayan Mommed Mursi

Ana dai yi wa 'yan jam'iyyar ta Yan Uwa Musulumi kallon a matsayin waɗanda suke da laifuka a can baya na ƙaddamar da ayyukan ta'addanci. Da kuma wannan lokaci na bayan bayan nan da suka yi mulki wanda a kan haka sabbin shugabannin suka yi shelar kame mutane kusan ɗari uku magoya bayan jam'iyyar.

Abdul Bar Zahram jigo ne a cikin jam'iyyar addawa da ake kiran yantacciyar jam'iyya ta Masar. Ya ce: ''ko ma ba saboda wannan kame ba, na mutane masu yawan gaske. Masar ta shiga wani hali wanda muke da fargaba na yi war sake faɗawa cikin mulkin kama karya amma ba mu fatan haka.''

Yawancin waɗanda ake tsare da su ana zarginsu da yin kira ga magoya bayansu da su tayar da fitina. A halin da ake ciki dai fargaban da ake da shi yazuwa yanzu shi ne cewar ka da waɗannan shugabannin su sake maimaita irin kura kurai da masu kishin addinin suka aikata. Tuni da ƙungiyar Tarrayar ƙasashen Afirka ta dakatar da ƙasar ta Masar daga cikinta yayin da ƙungiyar kare hakin bil Addama ta MDD ta ce ta damu da abinda ke faruwa na kame-kamen jama'a a Masar ɗin.

Daga ƙasa a a iya sauraron wannan rahoto haɗe da na zanga-zangar da aka yi a yau a Masar wanda Wakilinmu Mahmud Azare Yaya ya aiko mana da kuma sharhi a kan matsayin Isra'ila dangane da rikicin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe

Sauti da bidiyo akan labarin