Magoya bayan Mursi na ci gaba da gudanar da zanga-zanga | Labarai | DW | 20.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Magoya bayan Mursi na ci gaba da gudanar da zanga-zanga

Akallah mutane uku sun rasu yayin da wasu bakwai suka jikkata lokacin wata arangama tsakanin magoya bayan Mursi da kuma masu adawa da shi.

Kungiyar 'Yan Uwa Muslmi na ci gaba da gudanar da zanga-zanga a wannan Asabar domin neman a dawo da hambararren shugaban kasar Muhammad Mursi da sojoji suka yi wa juyin mulki. Shi dai Mursi ya lashe zabe a karkashin jagoranicn kungiyar ta 'Yan Uwa Musulmi, sai dai kuma sojoji sun kifar da gwamnatinsa a dai dai lokacin da yake cika shekara guda a kan karagar mulkin kasar, tare da kafa gwamnatin rikon kwarya, abin da ya janyo gagarumar zanga-zangar magoya bayansa ta tsawon kwanaki. Dubban magoya bayan Mursi ne dai suke gudanar da zaman dirshan a Masallacin Rabaa al-Adawiya dake birnin Alkahira, suna dauke da tutocin kasar da kuma hotunan hambararren shugaban. Wannan dai na faruwa ne a daidai lokacin da kasar ke tsaka da rikicin siyasa, inda bangarori biyu dake gaba da juna suka yi taho mu gama a tsakaninsu a daren ranar Juma'a, a zanga-zangar da aka bayyana da mafi girma tun bayan kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar. A kallah mutane uku ne suka rasa rayukansu yayin da wasu bakwai suka jikkata wanda hakan ya kawo adadin wadanda suka jikkata zuwa 34, yayin arangamar da magoya bayan Mursi da kuma masu adawa da shi suka yi.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal