1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Gwamnati ta sauke magadan gari

Salissou Boukari
June 27, 2019

A Jamhuriyar Nijar zaman taron majalisar ministoci da ya gudana a Larabar da ta gabata, karkashin jagorancin shugaban kasar Issoufou Mahamadou ya sanar da tsige magadan gari na biranen Agadez da Diffa.

https://p.dw.com/p/3LCLq
UN-Klimakonferenz 2017 in Bonn | Mahamadou Issoufou, Präsident Niger
Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar NijarHoto: Getty Images/AFP/P. Stollarz

Zaman taron ya kuma tsige shugaban karamnar hukumar mulki ta Chadakori cikin jihar Maradi kana ya soke wata majalisar karamar hukuma a jihar Dosso. Sanarwar ta taron majalisar ministocin ta ce jami'an gwamnati masu bincike da suka binciki yadda ake gudanar da aikin shugabancin birnin Agadez da Diffa da kuma karamar hukumar Chadakori a cikin jihar Maradi, sun gano irin tabargazar da aka tafka musamman ma kan abun da ya shafi tafiyar da harkokin kudi a wadannan hukumomi. Misali cikin da'irar birnin Agadez, binciken ya nuna cewa an yi ta bada kwangiloli ba bisa ka'ida ba, sannan an yi rufa-rufa domin boye wata tabargaza da aka yi da dukiyar al'umma musamman ma wajen kudin da mahukuntan birnin na Agadez ke kashewa da sunan gudanar da ayyuka, sannan ga tabargaza wajen sayar da filaye da bashi maras dalili.

A da'irar birnin Diffa kuwa binciken ya nunar cewa, magajin garin na Diffa na bayar da kwangiloli da suka sabawa ka'idojin bayar da kwangila, domin kuwa yana bayarwa ne ga danginsa, lamarin da ke haddasa rashin jituwa tsakaninsa da sauran al'umma. Haka kuma a karamar hukumar Chadakori da ke cikin jihar Maradi, an gano cewa a nan ma ana tafka ta'asa wajen tafiyar da tattalin arzikin karamar hukumar, domin babu tsarin tafiyar da fitar kudade da shigarsu wanda kuma hakan ya saba wa kudiri mai lamba 268 da 269 na kundin tafiyar da kananan hukukomi a Nijar.