1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bude taro kan sauyin yanayi a Madirid

Usman Shehu Usman LMJ
December 2, 2019

Kasashen duniya sun taru a birnin Madrid domin halartar daya daga cikin manyan taruka mafiya hada mutane a duniya, wato taro kan sauyi ko dumamar yanayi da aka yi wa lakabi da COP25.

https://p.dw.com/p/3U5JG
Spanien Madrid l PK Antonio Guterres vor der 25. UN-Klimakonferenz
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayin bude taron COP25Hoto: Getty Images/AFP/C. Quicler

Tun da fari dai an shirya za a gudanar da taron Chile ne, sai dai sakamkon rashin kammala shirin hukumomin kasar aka mayar shi zuwa Madrid babban birnin kasar Spain. Masu ruwa da tsaki kan muhallin dai, sun yaba da kokarin kasar Spain bisa daukar nauyin taron da ta yi, duk kuwa da cewa tun asali ba ita aka tsara za ta karbi bakuncinsa ba. Ministar muhalli ta Jamus Svenja Schulze ta bayyana godiyarta ga mahukuntan na Madrid, ganin cewa sun dauki nauyin taron cikin makonni hudu kacal da janye shi daga Chile. Masu zanga-zangar yaki da sauyi ko kuma dumamar yanayi a biranen kasashen duniya sun karu a bana fiye da ko wanne lokaci.

Tilas a hada hannu waje guda

Spanien Madrid l  25. UN-Klimakonferenz - Logo
Taron sauyi ko dumamar yanayi COP 25 a MadridHoto: Getty Images/P. Blazquez Dominguez

Sai dai acewar Ann-Kathrin Schneider, mamba a kungiyar kare mahalli da ke kasar Jamus, duk irin wannan gangamin da ake yi a duniya zai yi tasiri ne kawai idan har shugabannin siyasa suka dauki lamarin da gaske. Shi ma dai sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, ya bayyanan cewa yaki da sauyin yanayi abu ne da ke bukatar hada hannun waje guda, kana kasashen duniya su nuna da gaske suke yi, kama daga kamfanoni masu zaman kansu da wakilan cibiyoyin kudi da kungiyoyin fararen hula duk su tashi tsaye kan lamarin. Babbar matsala da yaki da sauyin yanayi ke fuskanta dai ita ce yadda kamfanoni masu fitar da hayakin da ke jawo dumamar yanayi suke ta jan kafa wajen daukar matakan gaske, sai kuma uwa uba yadda kasar Amirka da ke kan gaba a fannin masana'antu a duniya ta fice daga cikin yarjejeniyar kare mahalli wacce duniya ta cimma a Paris, sakamakon adawa da kudurin wanda shugaba Donald Trump ke yi, abin da ke zama babban hadari ga daukacin shirin kare mahalli.