Macron da Guelleh sun magantu kan Habasha
September 11, 2022Talla
Shugaba Emmanuel Macron ya ce kasarsa na cike da zumudin ganin samun dawamammen zaman lafiya a Jibuti da ma yankin Kahon Afirka baki daya, a yayin tattaunawarsu ta war tarho da shugaba Ismaïl Omar Guelleh.
Fadar Elysée ta ce burinta a samu kwanciyar hankali a karamar kasar duba da yadda tashe-tashen hankula ke kara kamari tsakanin gwamanati da dakarun 'yan aware da ke a makwabciyar kasar Habasha, lamarin da ke kara haifar da fargaba da karancin cimaka.
Faransa ta jibge dakarun sojinta akalla 1.500 a Djibouti a wani sansanin na musamman da ke zaman ko takwana.