Mace mai tukin jirgin ruwa a Kwango | Himma dai Matasa | DW | 17.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Mace mai tukin jirgin ruwa a Kwango

Viviane Peled na daf da zama mace ta farko matukiyar jirgin ruwa a kogin Kwango a Kinshasa.

Kongo Viviane Peled

Viviane Peled me tuka jirgin ruwa a Kwango

A ko wacce ranar Allah da safe da misalin karfe bakwai dalibai na hallara ne a makarantar koyar da nazarin ayyukan sifurin jiragen ruwa a Kinshasa ta CRFNI a yayin da Viviane Peled da take a makarantar har tsawon shekaru biyu da rabi domin kokarin zama Captain din jirgin ruwan. kazalika tana daya daga cikin mata hudu da ke wannan gwagwarmayar a ajinsu.

Mata na da mahimmanci ga harkar zirga-zirgar sufurin jiragen ruwa,na son cewar muddin mace za ta iya shugabantar kasa,to za ta iya jagorantar jirgin ruwa ke nan.

Viviane Peled na matukar burin wannan aikin a dai-dai lokacin da jagororin jiragen ruwa wato Captain basu da yawa a kogunan ruwan Kwango. Horaswar dai na bukatar bada kulawa sosai, wannan yana da mahimmanci saboda kogunan kasar Kwango suna da siradi sosai kama daga bishiyoyi, yashe bakin gaba wadanda ke kawo cikas ga harkokin sufurin jirgin ruwan.

Kongo Boot auf Kongofluss

Tuka jirgi a tekun Kwango

"Dukkan abinda nake a nan yana da muhimmanci, matasa aka sari basa son lissafi haka kuma abin yake a gare ni,to amma a nan na fahimci cewar irin mahimancn daya ke da shi, idan zaka tuka jirgi akwai wani abu da kake da bukatam, wannan kuwa shi ne Trigonometry don haka komai anan yana da mahimmanci wajen tukin jirgin ruwa".

Viviane dai na amfani da lokutan da bata aji wajen ziyartar mahaifiyar ta Marceline wacce ke kulawa da ita, bayan kaninta Shilo, A kusan shekaru uku Vivian ta bar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kana ta isa Kinshasa, tafiya ce mai hadarin gaske a yayin da a ke tafka yakin basasa a kasarta ta haihuwa.

Kongo Fluss Markt

Kasuwa a gabar tekun Kwango

Baya ga Iyayena, wannan horaswar tana mahimmanci a gare ni saboda na futo ne daga dangin da basu da hali,shi ne na yanke shawarar fara karatun tukin jirgin ruwa,daga karshe iyayena za su amfana da hakan.

Viaviane dai bata tsoro a ayin da take kokarin kammala karatunta a shekaru hudu masu zuwa tare da zamatowa Captain mace ta farko a Jamhuriyar Afirka taTsakiya.

Sauti da bidiyo akan labarin