Mace-macen yara ƙanana a Nijar ya yi ƙasa | Labarai | DW | 23.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mace-macen yara ƙanana a Nijar ya yi ƙasa

Ƙungiyar Save the Children ta ce daga yara 326 cikin dubu da suka riƙa mutu a shekarun 1990,ya koma 114 cikin dubu a shekara ta 2012.

Ƙungiyar ta ce Nijar ita ce a sahun gaba a cikin jerin ƙasashen da aka sami raguwar na mutuwar yara 'yan ƙasa da shekaru biyar tun daga shekarun 1990. A cikin wani rahoton da ta bayyana ƙungiyar ta ce a cikin ƙasashe 10 waɗanda suka yi nasarar rage yawan mace-macen ta hanyar yin riga kafi ga cututtukan da ke haddasa mutuwar yaran.

Sune ƙasashen Laberiya da Ruwanda da Indunisiya da Indiya da China da Masar da Tanzaniya ada kuma Mozanbik. Ƙasashen da ke a ƙarshe kuma a cikin ƙasashen 75 inda ƙungiyar ta yi bincike sune Haiti da Papua New Guinea da Equatorial Guinea.Ƙungiyar ta Save the Children ta ce Nijar ta rage mutuwar yaran ne da kishi biyu bisa uku.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Nasir Awal