Mace-mace a filin kwallon Kinshasa. | Labarai | DW | 12.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mace-mace a filin kwallon Kinshasa.

Wani hargitsi da ya wakana a filin kwallon kafa na birnin Kinshasa ya yi sanadiyar rasuwar mutane 15 daga cikin magoyan bayan TPM da ASV da ke karawa da juna.

Ture-ture da ya wakana a filin kwallon Kinshasa lokacin gudanar da wasa tsakanin ASV Club da Tout Puissant Mazembe da ke da tarin magoya baya a Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango ya haddasa mutuwar akalla mutane 15. Club din biyu dai suna karawar karshe ce, a rana ta shidda kuma ta karshe na gasar wasannin kwallon kasar na kakan farko da aka shirya.

Magoya bayan ASV Club sun kasa jure cin da club din Mazembe ke yi musu na daya da banza, har ma suka fara jefa duwatsu a filin kwallon, yayin daga nasu bangare jami'an 'yan sanda suka harba hayaki mai sa kwalla a kokarin shawo kan hargitsin, abun da ya haddasa ture-ture a filin kwallon dake cike makil da jama'a.

Daga nasu bangare gwamnan birnin na Kinshasa da ma ministan cikin gidan kasar, sun isa a babban asibitin da aka kai gawawakin tare da wadanda suna jikkata, domin gane idanunsu inda suka ba da tabbacin cewa bincike zai biyo baya.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe