Mace mace a bikin shiga 2013 a Abidjan | Labarai | DW | 01.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mace mace a bikin shiga 2013 a Abidjan

Turereniya a bikin shiga sabuwar shekara ta 2013 ta hadassa mutuwar mutane da dama a Abidjan na Côte d'ivoire. Wadanda suka jika na kwance a asibitoci domin samun magani.

Akalla mutane sittin sun rasa rayukansu wasu sama da hamsin kuma suka jikata a Abidjan babban birnin Côte d'Ivoire yayin wata turereniya da ta wakana lokacin shagulgulan shiga sabuwar shekara. Rundunar 'yan kwana kwana ta kasar da ke yammacin Afirka ta ce an garzaya da wadanda suka sami raunuka asibitocin Abidjan domin yi musu magani, cikin kuwa har da yara kanana.

Tururuwa da mazauna babban birnin Côte d 'ivoire suka yi a gaban kofar shiga filin kwalon Abidjan a jiya litinin da maraice domin shaidar da yadda bikukuwan za su gudana ne ta hadassa turereniya a cewar hukumomin kasar. Hutunan da tashar telebijin mallakar gwamnati ta nuna a wannan talatar sun nunar da gawawwakin mutane da aka tattake da kuma runfunan matan da aka kawo wa dauki.

Wannan dai shi ne karo na biyu da birnin Abidjan ta shirya bikin shiga sabuwar shekara a wani mataki na neman hada kawunan 'yan kasar bayan rikicin siyasa da ta fiskanta wanda ya yi lamshe rayukan mutane dubu uku.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi