Ma´amila tsakanin Jamus da Rasha | Labarai | DW | 13.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ma´amila tsakanin Jamus da Rasha

Shugaban Jamus Christian Wulff ya gana ta takwaransa na Rasha Dmitri Medvedev da zumar ƙarfafa ma´amila tsakanin Jamus da Rasha

default

Christian Wulff da Dmitri Medvedev

Sugaban ƙasar Jamus Christian Wulff, na ci gaba da ziyara aikin kwanaki huɗu da ya kai a Rasha.A yau ya gana da takwaransa Dmitri Medvedev a birnin Mosko, inda su ka tattana kan batutuwa dabamdaban da su ka jiɓanci hulɗoɗi tsakanin ƙasashen biyu.Wulff ya  buƙaci game ƙarfi da Rasha wajen yaƙi da ta´adanci da kuma ɗumamar yanayi.

A ɗaya wajen sugaban ƙasar Jamus ya yi kira ga humomin Kremlin su ƙara himmantuwa wajen kare haƙƙoƙin bani Adama.

Nan gaba  a yau shugaba Christian Wullf zai gana da Ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bani Adama na ƙasar Rasha.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Umaru Aliyu