Ma′aikata yan ci rani suna ganin ta-kansu a Saudi Arabiya | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 22.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Ma'aikata yan ci rani suna ganin ta-kansu a Saudi Arabiya

Jaridun Jamus sun maida hankalinsu ne ga matakin da hukumomin Saudi Arabiya suke dauka na koran baki yan ci rani daga kasar a yunkurin samarwa al'ummarsu wuraren aiki.

Jaridar Neue Zürcher Zeitung tace Saudi Arabiya ta shiga farautar ma'aikata yan ci rani. Gwamnati a Riad, inji jaridar, ta fara daukar wannan mataki ne domin maida harkokin tattalin arzkin Saudi a hannun yan kasa. To sai dai wannan kampe maimakon ya gyara, sai ma ya jefa tattalin arzkin cikin wani hali na tsaka-mai-wuya. Kasar dai ta fara samun karancin kayiyakin da aka saba baki suna jigilarsu, yayin da tsabtar garuruwa da biranen kasar take kara ja da baya.Yayin da rashin aikin yi a kasar ta Saudi ya kai kashi goma sha ukku cikin dari na al'ummrta miliyan 28, ma'aikata yan ci rani sun kai kashi daya cikin kashi ukku na wannan adadi. Jaridar Neue Zürcher Zeitung tace tun da hukumomin na Saudi Arabiya suka fara daukar matakin kamawa da koran baki, dimbin yan ci rani suka shiga wasan buya, suka ki zuwa wuraren su na aiki. Sakamakon hakan shine karancin kayan mararufi na yau da kullum da rashin ma'aikata a wuraren gine-gine ko masu kwashe shara.

Daga cikin ma'aikata yan ci rani da matakinn a Saudi Arabia ya shafe su, har da wadanda suka fito daga Habasha ko Eritrea. Jaridar Die Welt tace wadannan yan ci rani, musamman yan mata, sukan zama kamar dai bayi ga iyayen gidansu a kasar ta Saudi. Jaridar tayi tsokaci da mummunan halin da yaran gidan sukan fuskanta, inda suke aiki sau tari ba albashi sai wahala ga fyade ko gallazawa. Jaridar tace da yawa sukan bar kasashensu na asali ne zuwa daulolin Larabawa domin neman abin duniya, amma mafi yawansu sukan koma gida gara jiya da yau. Wasu sukan bace ko sama ko kasa, wasu kuma a maida gawarwakinsu gida.

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung tayi sharhi ne game da shirin Jamus na horad da jami'an tsaro na musamman masu yaki da aiyukan tarzoma na kasar Kenya. Jaridar tace ta hanyar horaswa da daurawa wannan runduna ta Kenya damarar makamai, duk kuwa da sanin aiyukan da take gudanarwa na rashin imanin kan yan Kenya, Jamus ta rufe idanunta ga manufofi na kare hakkin yan Adam. Jaridar Süddeutsche Zeitung tace ko da shike Kenya ita ce yar lelen Amirka a matakin yaki da aiyukan tarzoma a Afirka, matakin da ake tsara shi da tafiyar dashi daga nan Jamus, amma batun kare hakkin dan Adam fa? Tun bayan harin 11 ga watan Satumba na shekara ta 2001 a Amirka, kasar take farautar yan tarzoma a kasashen Afghanistan da Pakistan da Yemen, amma a yanzu tafi maida hankalinta ne ga nahiyar Afirka, inda a can Kenya ta zama dandalin wannan yaki.

Julius Malema

Julius Malema shugaban jam'iyyar EFF a Afirka Ta Kudu

Jaridar Tageszeitung ta duba halin siyasa a Afirka Ta Kudu, inda tace yanzu dai kofa ta bude wa mai tsananin kishin kasa, Julius Malema a game da fara kampe domin cika burinsa na zama shugaban kasa a zaben shekara ta 2014. Wani kotu a garin Polokwane farko wannan mako ya dage shari'ar da ake yiwa dan kishin kasar saboda zargin cin rashawa har sai watan Satumba na shekara ta 2014. Hakan inji jaridar Tageszeitung, zai baiwa shugaban jam'iyar ta EFF damar tafiyar da kampen neman zama shugaban kasar Afika ta kudu a zaben da za'a yi a watan Aprilu na shekara ta 2014. Shekaru biyu da suka wuce jam'iyar ANC dake mulki ta kori Malema daga cikinta saboda zargin bata suna, bayan da aka ce yana da laifi tattare da cin rashawar kudi Rand miliyan hudu. Sai dai masharhanta suka ce duka wadannan abubuwa suna samuwa ne kansa saboda sabanin dake tsakaninsa da shugaban kasa, kuma shugaban jam'iyar ANC, Jacob Zuma.