Ma'aikata sun bai wa hamata iska a filin wasan Barcelona
October 11, 2024Gomman masu aikin gina sabon filin wasan Camp Nou na kungiyar kwallaon kafa ta Barcelona sun bai wa hamata iska a ranar Juma'a kamar yadda 'yansanda suka tabbatar wa kamfanin dillancin Labarai na AFP.
Shida daga cikin mutum 20 zuwa 30 da suka dambata sun samu raunuka kafun shiga tsakani da jami'an tsaro suka yi.
Babu wanda aka tsare kuma babu wanda aka tuhuma da wani laifi ya zuwa yanzu acewar majiyar da ta tabbatar da labarin.
Karin bayani:Wasanni: Barcelona na tsaka mai wuya
Kafafen yada labaran Sfaniya sun ruwaito cewa wasu daga cikin ma'aikatan sun yi amfani da katakin aiki a matsayin makami wajen korar abokan fadan nasu da gudu.
Karin bayani:Messi zai koma Inter Miami na Amirka
Rahotanni sun bayyana cewa dan kwangilar da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta dauka ya gina mata sabon filin wasan ya kori wadanda suka bai wa hamata iskan daga aiki.