1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga ma'aikata a yankin Hong Kong

Binta Aliyu Zurmi MNA
December 2, 2019

Daruruwan ma'aikata a Hong Kong sun shiga zanga-zanga da za ta dauki tsawon mako guda ana yi don nuna goyon bayansu ga masu rajin tabbatar da dimukuradiyya a yankin.

https://p.dw.com/p/3U6oj
China Hongkong Proteste
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Ng Han Guan

Masu zanga-zangar sun bayyana cewa za su rika fitowa a kullum daidai lokacin da ma'aikata kan fita don yin hutu da kuma cin abincin rana.

Zanga-zangar dai na mai kokarin janyo hankalin ma'aikata musamman ma wadanda ke aiki a fannin jarida don su yi amfani da damarsu ta kara yada lamarin yadda ya kamata.

Wannan na zuwa ne bayan nasarar da suka samu a zaben da aka gudanar a yankin a watan da ya gabata. Ko a ranar Lahadi ma jami'an 'yan sanda sun watsa wa wasu masu zanga-zangar hayaki mai sa hawaye, a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa ofishin jakadancin Amirka don yin godiya kan taimakon da Washington ta ba su.