Lumumba: Mafarkin Kwango ya ragargaza | Tushen Afirka: mutanen da suka taka rawa a tarihin Afirka | DW | 31.07.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Tushen Afirka

Lumumba: Mafarkin Kwango ya ragargaza

Daga ma'aikacin aike sakonni zuwa firaminista a cikin shekaru kalilan: Patrice Lumumba ya saka karfinsa cikin yaki da Turawa 'yan mulkin mallaka a gaban duk wani kalubale.

Rayuwarsa: 

Patrice Émery Lumumba dai an haife shi a ranar 2 ga watan Yuli na shekara ta 1925, a wani kauye da ake kira Kasai. Bayan karantunsa na firamare ya zauna a Stanleyville Kisanganin, a farkon shekarun 1940 kafin ya isa a Lepoldville babban birnin kasar na waccan lokaci wanda yanzu ake kira da sunan Kinshasa. Ya zama ma'akacin aike sakonni na Poste. Ya zama firaministan Kwango wacce ta samu 'yanci a ranar 30 ga watan Yuni na shekara ta 1960. Sai dai ba a dade ba aka yi masa juyin mulki. An kashe Patrice Lumumba a Lumumbashi tsohon birinin da ake kira (ex-Élisabethville) da ke a yakin Katanga, a ranar 17 ga watan Yuni na shekara ta 1961.

Ya shahara saboda gwagwarmayyarsa ta samun 'yancin kan Kwango da kuma fafutukarsa ta a mutu ko a yi rai a game da batun 'yanci, ya sa ya yi suna har a ketaran Kwangon.

•A ranar 30 ga watan Janeru na shekara ta 1960 jawabin da ya yi na samun 'yancin kai an rika yada shi ko ina a duniya, "Babu wani dan Kwango da zai manta da wannan rana ta 'yanci, wanda aka samu ta hanyar zubar da jini". Irin kalaman da Lumumba ya bayyana a gaban sarkin Beljiyam.

•Lumumba a tsawon rayuwarsa ya yi ta yin rubuce-rubuce a game da wasu al'amuran Kwango da ma nahiyar Afirka. Kuma ko bayan shi sauran manyan 'yan bokon Afirka sun rika yin koyi da irin fafutukarsa ta yaki da turawan mulkin mallaka. Kamar su Aimé Césaire (Une saison au Congo, 1966).     

 

A dubi bidiyo 01:53

Patrice Lumumba

Wasu daga cikin kalamansa:

"Bama adawa da kowa, amma muna adawa da zalunci da rashin gaskiya da danniya, kuma rashin bai wa kowa hakkinsa daidai da nuna fifiko na mulkin mallaka, sune suka janyo wa kasashen Turai kyama."

«Za mu fara wata sabuwar fafutuka wacce za ta kai kasarmu ga hanyar samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba. Mu mai da Kwango cibiyar Afirka baki daya.»

«Azabatarwa da duka da azaba ba za su taba sa na nemi afuwa ba, na gwammace na mutu da mutunci na.»

 

Rudanin da aka rika samu a game da Lumumba:

Tambayoyi da ke tsakiyar wannan rudani sune: Wa ya kashe Patrice Lumumba?

A shekara ta 2002 gwamnatin Beljiyam ta nemi afuwa ga iyalensa. Sai dai wasu na cewar kokowar neman 'yancin Kwango wanda a kansa aka kashe mutane da dama cikin tashin hankali, ya sa martaba da darajar Lumumba sun zube a idon duniya tamkar lamarin ya bata masa suna.

Karkashin shirin na musamman da DW kan tsara na Tushen Afirka bisa tallafi na gidauniyar Gerda Henkel.

Sauti da bidiyo akan labarin