1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban kasar Burazil sai dawo siyasa

Zulaiha Abubakar
August 4, 2018

A kasar Burazil jam'iyyar adawa ta Workers Party ta tsayar da Luiz Inácio Lula da Silva, da ke daure a gidan yari a matsayin dan takaran ta na shugaban kasa a zabe mai zuwa

https://p.dw.com/p/32dDP
Brasilien Präsident Luiz Inacio Lula da Silva Amtseinführung in Brasilia
Hoto: O. Kissner/AFP/Getty Images

Jam'iyar ta tsayar da fitaccen jagora Luiz Inacio Lula da Silva a matsayin wanda zai yi mata takarar shugabancin kasar duk kuwa da cewar yana tsare a gidan yari sakamakon zargin  sa da cin hanci. Masu ruwa da tsakin jam'iyyar sun sanar da hakan ne a yau yayin wani taron jam'iyya da suka gudanar a birnin Sao Paulo a wannan Asabar, jim kadan bayan karanta wata wasika wace Lula da Silva ya aiko wa magoya bayansa daga gidan yari in da yake kara jaddada bukatar dawo da mulki irin na demokradiyya a kasar ta Brazil. A taron jam'iyyar dai wasu mutane kusan 2000 na dauke da mutum mutumin Lula da Silva tare da kiraye-kirayen sunan sa suna jinjinawa gwarzon nasu.