Litattafan tarihi na Timbuktu a fasahar zamani | Zamantakewa | DW | 07.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Litattafan tarihi na Timbuktu a fasahar zamani

Wata kungiya mai zaman kanta mai sunan "SAVAMA DCI" a Mali ta fara alkinta litattafen tarihi da masu kaifin kishin Islama suka niyar lalatawa a arewacin kasar a lokacin da garin Timbuktu ya fada hannunsu.

Tsofin litattafai na rubutun hannu na Timbukutu

Tsofin litattafai na rubutun hannu na Timbukutu

A cibiyar Kungiyar "SAVAMA DCI" da ke Bamako ana aiki ba dare ba rana don ganin cewar an ceto duk rubuce-rubuce da masana addini Musulunci suka yi a Timbuktu shekaru aru-arun da suka gabata.Baya ga gyara litattafan da suka lalace, jami'ai na daukan hotonsu don sanyasu a na'ura da nufin adanasu. Dama dai kalilan daga cikin rubuce-rubucen aka yi nasarar jigilarsu zuwa babban birnin Mali bayan da masu kaifin kishin addini suka rusa wuraren tarihi.  

Litattafai na Timbukutu wadanda aka sake cetowa daga hannun 'yan ta'adda

Litattafai na Timbukutu wadanda aka sake cetowa daga hannun 'yan ta'adda

Shugaban wannan kungiya Abdel Kader Haidara ya nuna farin cikinsa dangane da wannan ci gaban da aka samu."A baya dai, rubuce-rubucen na warwace ne a cikin akwatuna a cikin mummunan yanayi cike kuma da kura. Amma a yanzu cikin ikon Allah an tsabtace kashi 70 daga cikin 100 na wadannan litattafan, sannan a fassarasu zuwa Faransanci, an ajiyesu cikin kwakabe tare da jerasu."Kafin karshen wannan shekara ta 2017 ne ake sa ran kammala aikin na adana rubuce-rubucen na tarihi. Sannan kuma a kara diban wani wa'adi don amfani da na'urori wajen alkintasu. Da farko dai Kungiyar SAVAMA DCi ta fara amfani da na'urori biyu, amma a yanzu tana da na'u'rori 12, sannan ma'aikatanta sun fara kwarewa a wannan fanni.