1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Limbourg ne sabon daraktan kafar watsa labaru ta Deutsche Welle

March 15, 2013

An zabi Peter Limbourg a matsayin sabon babban daraktan Deutsche Welle. Valentin Schmidt shugaban hukumar kula da ayyukan kafafan watsa labaru ya ba da wannan sanarwa bayan wani taro a birnin Berlin.

https://p.dw.com/p/17ymK
Peter Limbourg, derzeitiger Informationsdirektor von ProSiebenSat.1 TV Deutschland, wird neuer Intendant der Deutschen Welle und Nachfolger von Erik Bettermann, dessen Amtszeit am 30. September endet.
Hoto: picture-alliance/dpa

Hukumar kula da ayyukan kafafan yada labaru mai membobi 17 ta zabi Peter Limbourg wanda shi ne daraktan hadakar tashoshin telebijin Jamus na ProSiebenSat.1 masu zaman kansu, a matsayin wanda zai gaji shugaban Deutsche Welle mai barin gado Erik Bettermann. A ranar 30 ga watan Satumba Bettermann mai shekaru 68 yake kare wa'adin aikinsa. Tun a shekarar 2001 yake jagorantar kafar watsa labarun na Jamus zuwa ketare kuma ya taka rawa wajen sauye sauyen da aka yi mata.

Mutane 14 suka kada kuri'ar amincewa da sabon daraktan, daya ya nuna adawa sannan biyu suka yi rowar kuri'unsu a zagayen farko kuma daya tilo na zaben.

Erik Bettermann
Bettermann ya kasance shugaban DW tsawon shekaru 12Hoto: DW

"Peter Limbourg na da kwarewar da ake bukata na karfafa Deutsche Welle a matsayin wata kafar yada labaru ta zamani tare kuma da inganta matsayin Jamus a fagen watsa labaru na kasa da kasa. Kwararren dan jarida ne dake da masaniyar siyasar kasa da kasa wanda ya nakalci harsuna daban daban, ya na da kwarewa ta tafiyar da ayyukan watsa labaru", inji Valentin Schmidt shugabar hukumar kula da ayyukan kafafan watsa labaru.

Sabon daraktan zai kara inganta ayyukan sassan harsunan DW

Limbourg mai shekaru 52 ya gode wa hukumar da wannan amincewar da ta nuna masa. "Bani wannan dama ta taka muhimmiyar rawa kan yadda duniya ke daukar kasarmu, zai zama wani babban kalubale da zan yi kokarin tinkara a cikin shekaru masu zuwa. Tun ina matashi a ketare, shirye shiryen Deutsche Welle sun zama wani bangare mai daraja a rayuwata. Tare da hadin kan dukkan ma'aikata maza da mata, ina fatan inganta ayyukan jarida na Deutsche Welle da shirye shiryen sassan harsuna daban daban da kuma sassan watsa labaru. Ci-gaba da karfafa hadin kai da kafofin watsa labarun jihohi na ARD da ZDF na zaman wani buri a gare ni da zan cika."

Bayan ya yi wa kasa hidima na soji, Limbourg ya yi karatun jami'a a fannin kimiyar shari'a a Bonn, inda a shekarar 1987 ya ci jarrabawar farko ta kasa ta fannin shari'a. Daga 1988 zuwa 1989 ya yi aikin sa kai a kamfanin dillancin labarun telebijin na Jamus wato DFA a biranen Bonn da London. Bayan yada zango a matsayin mai aike wa da rahotanni a tsohuwar Jamus ta Gabas a birnin Leipzig, tun a shekarar 1990 ya kuma zama wakilin DFA na Turai da NATO da kuma SAT.1 a birnin Brussels. A 1996 ya karbi ragamar ofishin ProSieben a Bonn, a 1999 aka nada shi mataimakin babban editan tashar telebijin ta N24 kuma shugaban sashen siyasa na ProSieben, a 2001 aka kara masa tashar SAT.1. A shekarun 2004/05 da 2008/09 Limbourg yayi aiki a matsayin daraktan Pool TV, wata hadakar kamfanonin watsa labaru masu zaman kansu a Berlin. Tsakanin 2008 da 2010 ya karbi ragamar babban edita na shirin N24. Tun a 2008 ya zama babban mai gabatar da labaran SAT.1, sannan a 2010 daraktan watsa labaru na ProSiebenSat.1 TV a Jamus kuma mataimakin shugaban kula da labarai da batutuwan siyasa.

Limbourg shi ne shugaban alkalan dake ba da lambar yabo ta 'yan jarida ta majalisar dokokin Jamus Bundestag, memba ne a kungiyar alkalai masu ba da kyautar Axel Springer ga 'yan jarida matasa, mai ba da shawara ne a hukumar watsa labaru ta babban taron Bishop Bishop na Jamus.

Haifaffen birnin Bonn, Limbourg ya girma a biranen Rom, Paris, Athens da kuma Brussels. Yana da aure da 'ya'ya uku.

Mawallafa: Johannes Hoffmann / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi