1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Limaman addinai sun ja hankali kan fitinar zabe

Uwais Abubakar IdrisFebruary 5, 2015

Jagororin addinai a Najeriya za su nusar da 'yan Najeriya kan bukatar kiyaye hargitsin zabe

https://p.dw.com/p/1EWGy
Symbolbild Gewalt in Nigeria
Hoto: SEYLLOU DIALLO/AFP/Getty Images

Manyan malaman addinin mususlunci da na Krista sun amince da aiki tare domin kaucewa afkuwar rigingimu a zaben da ke tafe a Najeriya, ta hanyar amafani da tasirin addini wajen wayar da kai da ma fadakar da mabiyansu illar da ke tattare da hakan.

Malaman manyan addinan da suka hadu a teburi guda sun yi kokarin shaidawa juna gaskiya a kan abin da suka ce sun hango a matsayin babbar barazanar da dole su yi mata tarabe-tarabe.

Munin abinda ya faru a zaben 2011 da ya sanya babu mai fatan sake ganin faruwarsa, ya sanya da dadewa malaman addinan suka yi kokarin fahimtar da junansu. Ga Sheikh Ahmed Gumi da ke Kaduna ya kashedi ga mabiya don abinda ka iya biyo baya day ace yaudara ce daga ‘yan siyasa domin cid a rigar addini.

Sanin tasirin da addini ke da shi a Najeriya ya sanya sassan biyu gudanar da wannan taro a dai dai lokacin da ake kara nuna damuwa a kan zaben.