1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya ta buƙaci agajin Majalisar Ɗinkin Duniya

August 13, 2014

Majalisar dokokin Libiya ta nemi Majalisar Ɗinkin Duniya da ta kare farar hula da yaƙin da ake yi a ƙasar ya rutsa da su.

https://p.dw.com/p/1CuOi
Libyen Tobruk Parlament 2.8.2014
Hoto: Reuters

Majalisar ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da wani daftarin ƙudiri wanda ke ba da izinin kwance ɗamarar dakarun sa kai na ƙasar.

Wannan doka ta shafi ƙungiyoyin mayaƙan sa kai waɗanda ke da alaƙa da 'yan aware na garin Misirata. Sai dai wani abin da ba a a tabbas a kansa shi ne cewar ko majalisar na da ƙarfin ikon zartas da wannan doka ga gwamnatin da har yanzu ba ta da cikakken iko wajen tafiyar da harkokin tsaro a ƙasar.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Suleiman Babayo