Liberiya: Sanata George Weah na kan gaba | Labarai | DW | 14.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Liberiya: Sanata George Weah na kan gaba

Hukumar zaben Liberiya ta NEC ta sanar da cewar 'yan takarar neman shugabancin kasar guda biyu ne suka bada babbar rata a gaban sauran 'yan takarar 18 da ke neman shugabancin kasar.

Libera, George Weah (Getty Images)

Dan takara sanata George Weah na Liberiya

Shugaban hukumar zaben kasar Jerome Korkoya ya sanarwa taron manema labarai cewar, Sanata George Weah tsohon shahararren dan wasan kwallon kafar na Afirka shi ne ke kan gaba da kashi 39,6 %, yayin da mataimakin shugaban kasar ta Liberiya Joseph Boakai,  ke bi masa da kashi 31,1 %, mai bi musu na uku shi ne lauya Charles Brumskine da kashi 9,3 % kana tsohon jagoran kamfanin Coca-Cola na Afirka ke da kashi 6,7 %.

Wannan sakamako dai ya shafi kashi  33,71% na runfunan zaben kasar 5.390. Daga cikin jihohin kasar 15 Sanata George Weah na kan gaba a jihohi 12, ciki kuwa har da Monrovia babban birnin kasar, inda yake Sanata tun daga shekara ta 2014.

Birnin Monrovia shi kadai na a matsayin kashi 40 cikin 100 na yawan al'umma kasar miliyan biyu da dubu 100 masu yin zaben. Sai dai wannan sakamakon na a matsayin na wucin-gadi ganin cewa bai ma kai na rabin runfunan zaben ba.