Leken asirin Majalisar Dinkin Duniya | Labarai | DW | 26.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Leken asirin Majalisar Dinkin Duniya

Wata mujallar Jamus ta zargi Hukumar Leken Asirin Amirka da satar bayanai a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya.

Mujallar Der Spiegel da a ke bugawa a nan Jamus, ta yi zargin cewar, Hukumar Leken Asirin Amirka ta saci bayanai daga hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York. Mujallar ta yi ikirarin cewar, ta ga wasu bayanan sirrin da ke nuna cewar, hukumar ta nadi wasu bayanan sirri ta hanyar na'urar bidiyo daga hedikwatar ta Majalisar Dinkin Duniya yayin da majalisar ke gudanar da wasu manyan taruka. Idan za a iya tunawa dai, badakalar da ta shafi bayanan sirrin da Hukumar Leken Asirin Amirka ke samu, ta taso ne bayan da Edward Snowder ya kwarmatasu ga jaridar Guardian ta Birtaniya. Hakanan a baya bayannan kuma, wani abokin huldarsa, kana dan jarida David Miranda, shi ma jami'an tsaron Birtaniya sun tsareshi na kimanin sa'oi tara a filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa na Heathrow da ke birnin na London, a makon jiya saboda abin da jami'an suka ce ya shafi wasu muhimman bayanai, harma Mirandan ya yi tsokaci:

Ya ce "Sun yi mini tambayoyin da suka shafi rayuwata baki daya, kana suka dauke mini na'urar Computer ta, da na'urar da nake wasanni, game da wayar salulata da kuma dukkan abin da yake tare dani."

Tun da dadewa ne dai, Amirka ta cimma yarjejeniya tare da Majalisar Dinkin Duniya game da cewar, ba za ta yi leken asiri a kan ayyukan da majalsar ke gudanar wa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Mohammad Nasir Awal