Lebanon zata zama dandali na biyu na rikicin Siriya | Siyasa | DW | 22.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Lebanon zata zama dandali na biyu na rikicin Siriya

Al'ummar Lebanon suna ci gaba da nuna tsoron makomar kasarsu bayan tashin hankalin da ya biyo bayan kisan Janar Hasasan

Kisan da aka yiwa Janaar Wissam al-Hassan, dan darikar Sunni ranar Jumma'a, nan da nan ya zama sanadin tayar da rikici mai tsanani a kasar ta Lebanon, abin da ya sanya tsohon Pirayim minista Saad Hariri yayi kira ga gwamnatin ta Lebanon gaba daya tayi murabus, saboda ta kasa daukar matakin hana kashe babban jami'in na yan sanda ko kuma dakatar da tashe-tashen hankulan da suka biyo baya. A birnin Tripoli dake arewacin kasar, inda nan ne yan darikar Sunni suka fi yawa, kuma wurin da ya zama matattarar masu adawa da shugaban Siriya, Bashar al-Assad, tashin hankalin ya kai ga mutuwar mutane da dama. A birnin Beirut an jiwa mutane masu yawa rauni, lokacin dauki ba dadi tsakanin matasa masu tashin hankali da jami'an tsaro. Majiyoyi suna kyautata zaton cewar an kashe al Hassan ne saboda a watan Agusta, bayan bincike mai tsanani, hukumar da yake jagoranta ta tsaron cikin gida, ta kama wani tsohon minista dake da dangantaka ta kurkusa da shugaban Syria Bashar al-Assad. Al-Hassan ya kuma jagoranci bincike game da mutuwar tsohon Pirayim ministan Lebanon, Rafik al-Hariri, wanda shima a shekara ta 2005 ya rasa ransa sakamakon bom da aka boye cikin mota, inda a sakamakon wannan bincike, aka zargi yan Hisbolah da dama da laifin kisan. Lokacin jana'izar al-Hassan, shugabanin Lebanon sun yi kira ga jami'an tsaro su gaggauta gano wadanda suke ga alhakin kisan jami'in a kuma gurfana dasu gaban shari'a. Shugaban kasa, Michel Suleiman yace:

"Ina kira ga hukumomin shari'a a kasarmu, kada wani abu ya basu tsoro, saboda al'ummar Lebanopn suna bayansu. Ina kira ga jami'anm tsaro su tsaya sosai kan aiikin su, ina kuma kira ga yan siyasa da gwamnati kada su yi kokarin boye duk wasu aiyukan na marasa son kasarmu da masu aikata manyan laifuka."

J

Libanon Beirut Beerdigung al Hassans

Jana'izar marigayi Wissam al-Hassan

im kadan bayan jana'izar, Pirayim minista mai ci, Najib Mikati yayi tayin murabus daga mukaminsa, amma shugaban kasa Micchel Suleiman ya nemi ya ci gaba a mukamin, domin hana Lebanon ta tsunduma gaba daya cikin halin yakin basasa.

Halin da ake ciki a kasar Siriya, ya watsu zuwa cikin kasar ta Lebanon, inda tuni Syria din take da ruwa da tsaki game da siyasa a cikin kasar. A Tripoli mai tashar jiragen ruwa, magoya baya da masu adawa da shugabannin Siriya suna ci gaba da yaki da junan su, yayin da mazauna sauran yankunan kasar suke kara baiyana tsoron cewar Lebanon zata zama dandali na biyu na yakin Syria. Wani mutum dake baiyana rashin jin dadin sa a game da halin da Lebanon din take ciki yace:

Najib Mikati Premierminister Libanon UN

Pirayim ministan Najib Mikati

"A Lebanon mun kai matsayin da tilas ne mu fadi cewar yanzu wajibi ne a dauki matakan da suka dace, saboda tuni muna ji, muna gani kasar mu tana kara tsunduma cikin rudami. Sannu a hankali ana kwace mana yanci da hakkinmu. Kashe Janar Wissam al-Hassan babban koma-baya ne a garemu."

Wani masani kan al'amuran gabas tsakiya, Hisham Khouri yace kashe Wissam al-Hassan da aka yi bai zama abin mamaki ba, saboda wannan wani matakine dake nuna fadadar abin dake gudana a Siriya tsawon watanni goma sha tara.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Halima Balaraba Abbas