1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Lebanon za ta yi shekaru da radadin tattalin arziki

December 25, 2021

Shugaba Aoun na Lebanon ya ce halin da kasar ke ciki na bukatar sai ta kwashe shekaru kafin ta farfado daga rugujewar tattalin arzikin da ya yi mata dabaibayi.

https://p.dw.com/p/44pMY
Libanon | TV Ansprache Präsident Michel Aoun
Hoto: Lebanese Presidency/Handout/AA/picture alliance

Shugaban Lebanon Michel Aoun ya ce kasar na bukatar shekaru shida zuwa bakwai kafin ta samu ta murmure daga matsin tattalin arzikin da take ciki a yanzu haka. Shugaban ya fadi haka a wata hira ta talabijim da aka yi da shi a ranar Juma'a.

Tun a shekara ta 2019 ne tattalin arzikin Lebanon ya fara rugujewa bayan da basussuka da rikicin siyasa suka taru suka yi wa kasar daurin huhun goro, lamarin da ya jefa kasar cikin matsalar tattalin arziki mafi muni tun bayan yakin basasa na shekarun 1975 zuwa 1990.