Sunkin burodi daya a Lebanon ya kai Naira 1800
June 22, 2021Talla
A yanzu gwamnati ta ce za a rika sayar da karamin burodi kan kudi Fam 3.25 kwatan-kwacin Naira 1,800. Hukumomin Lebanon sun ce an samu wannan kari ne a sakamakon janye tallafin da babban bankin kasar ya yi a kan sikari wanda ya haifar da tsadar kayayyakin da ake sarrafa burodi da su.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta Lebanon ke fama da karayar tattalin arzikin da Bankin Duniya ke cewa an yi kusan shekaru 150 wata kasa ta duniya ba ta fuskanci irinsa ba.