Lebanon: Sabuwar gwamnati na fuskantar barazana | Siyasa | DW | 14.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Lebanon: Sabuwar gwamnati na fuskantar barazana

Bayan da ta samu amincewar majalisar dokokin kasar, Sabuwar gwamnatin Lebanon na fuskantar tarin kalubalen wanda samo bakin zarensu na zaman zakaran gwajin dafin dorewa ko rushewarta.

Duk da cewa Sabuwar gwamnatin ta firaminista Hassan Diab ta samu amincewa da gagarimin rinjaye a majalisar, yadda 'yan majalisa 63 daga cikin 84 ne suka amince da ita, sai dai  rashin amincewar da  'yan  jam’iyyar Mustaqbal ta Rafik Hariri tsohon firaminista kasar da wasu kananan jam’iyyu suka yi wa gwamnatin, babar alama ce da ke nuni da cewar,har yanzu da sauran rina a kaba, dangane da samo bakin zaren warware dambaruwar siyasar kasar da aka shafe watanni biyu ana yi. Ban da wannan kalubalen na 'yan siyasa, matasa masu rajin samar da sauyi na ganin har yanzu ba ta canja zani ba, idan aka yi la'akari da tsarin gamin gambiza tsakanin 'yan siyasa da kwararraru da aka bi wajen kafa gwamnatin, lamarin da ya sanya ake ci gaba da yin zanga-zangar neman Hassan Diab din da ya sauka daga mukamin.

Tattalin arzikin Lebanon na fuskantar barazanar durkushewa saboda rikicin siyasar

Batun durkushewar tattalin arzikin kasar da ya kai ga bankuna suka kasa biyan masu ajiya kudadansu na ajiya, dai shi ne batun da ya fi tayar wa da gwamnatin ta Diab hankali, to sai dai kamar yadda sabon ministan kudi a gwamnatin Gazi Waznah ke gani, an fara gano bakin zaren wannan matsalar: "Taron da muka gudanar da asusun lamani na duniya kan rancen da ya yi alkawarin zai ba mu,da kuma sake garambawul a tsarin lokacin da za mu biya basusukan da ke kanmu, babbar alama ce da ke nuna irin kamun ludayin wannan gwamnatin."

To sai dai kamar yadda Tony Farah,wani mai fashin bakin siyasa a kasar ke kashedi shi ne,babu ta yadda za a yi a samun nasarar magance matsalolin tattalin arzikin kasar, muddin ba a samu cikakken hadin kan bangarorin siyasa da na addinin kasar ba. " Taimakon kudade da rancen da za,a ba mu yana da sharadi, sun ce ba za su yi mana komai ba, sai mun sasanta da junanmu, domin haka ne zai ba su tabbacin cewa ba za a koma gidan jiya wajen kashe kudaden kasar wajen karfafa jam,iyyar siyasa ko wani bangaren addini ba, sai idan mun yi haka ne za mu iya fita.

Sauti da bidiyo akan labarin