Boren kin jinin gwamnati na kara zafi a Lebanon
December 16, 2019Talla
Rahotanni sun ce masu boren sun jefa kwalaben ruwa da sauran ababen jifa ga jami'an tsaron, lamarin da ya harzuka su inda suka yi amfani da mesa da hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa masu boren.
Wannan lamarin na zuwa ne 'yan awowi kalilan bayan da jami'an tsaro sun yi amfani da harsasan roba wajen tarwatsa masu zanga-zanagar lamarin da ya rauwanata akalla mutane 36.
Tun a ranar 17 ga watan Oktoban wannan shekarar ne dai bore da kin jinin gwamnati suka barke a kasar ta Lebanon tare da zama musabbabin marabus din Firaminista Saad Hariri, to amma sai dai tun sdaga lokacin kawo yanzu majalisar dokokin kasar ta kasa samun wani sabon firaministan da zai karbi jan ragamar gwamnatin kasar.