Layin dogo daga Habasha zuwa Djibouti | Zamantakewa | DW | 05.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Layin dogo daga Habasha zuwa Djibouti

Kasar Habasha ta tasamma bunkasa inda yanzu haka ta kaddamar da hanyar jirgin kasa mai sauki don safara zuwa Djibouti da ke makwabtaka

Tashar jirgin kasa daga birnin  Addis Ababa zuwa birnin Djibouti da ke a gabar teku na da tazara ce ta kilomita 600 sannan za a rika safara ta fasinja da kaya tsakanin wadannan kasashe biyu makwabtan juna wato Habasha da Djibouti.

 

Aikin da ya lashe sama da Dala miliyan dubu uku kashi 70 cikin dari na sa kasar China ce ta dauki nayi yayin sauran kashin gwamnatin Habasha. Tafiyar kwanaki uku  a mota ta koma sa'oi goma zuwa sha biyu a jirgin kasa. Sannan tafiyar za ta fi sauri idan jirgin kasan na dauke ne da fasinja a cewar Makonnen Getachew  manajan aikin layin dogon.


Ya ce "Jirgin fasinja na tafiya da gudun kilomita 120 cikin sa'a guda jirgin dakon kaya zai gudun kilomita 90 cikin sa'a guda amma a karon farko zai yi tafiya kilomita 70 zuwa 80 cikin sa'a guda a matsayin gudun sa na karshe da aka tsara"
Wannan jirgi da za a sanya bisa layin dogo zai rika daukar fasinja 2800 kuma zai kai kawo sau biyu a rana, layin dogon dai za a fi dakon kaya ne tsakanin kasa da kasa. Kasancewar kasar ta Habasha ta dogara ne kashi 90 cikin dari da gabar teku a Djibouti wajen shigar da kaya da ma fitar da su. Za a rika safarar motoci da mashina da kayan sawa da fatu da kayan abinci.


Dereje Tefera,shugaban sashin huldar sadarwa a kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Ethopia ko Habasha ya yi karin haske kan alfanun wannan layin dogo a fiskar tattalin arziki.

Ya ce“ ya kasance mahada tsakanin Habasha da Djibouti da sauran kasashe makota
wannan zai rage kudin da ake kashewa a harkar sufuri da ma takaita lokaci, ga rashin gurbata muhalli saboda amfani da makamashi da ake sabintawa.

 

Kasar ta Habasha dai ta sadaukar da daya daga cikin madatsar ruwanta dan samar da hasken wutar lantarki ba katsewa a wannan aiki. Shekaru uku dai aka dauka na aikin na layin dogon tsakanin kasashen na Habasha da Djibouti, aikin da ke wa kallo na bunkasa tattalin arziki mai tsari a Afirka.