Laurent Gbagbo zai gurfana a gaban kotun duniya ta ICC. | Labarai | DW | 19.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Laurent Gbagbo zai gurfana a gaban kotun duniya ta ICC.

Kotun duniyar da ke hukunta man'yan laifukan yaƙi da ke a birnin Hage na zargin tsohon shugaban na Cote d'Ivoire da aikata kisan gilla a kan farar hula a lokacin zaɓe.

Laurent Gbagbo ɗan shekarun 67 da haifuwa ana tuhumarsa da aikata man'yan laifukan guda huɗu, waɗanda suka haɗa da na kisan gilla da fayɗe, da kuma wasu laifukan a lokacin zaɓen da aka gudanar a shekarun 2010 zuwa 2011.

A ƙarshen zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar wanda a kansa ya ƙi amincewa da nasarar' da shugaba Alassane Ouattara ya samu a cikin watan Nuwanba shekara ta 2010.A wannan zama kotu zata yi ƙokarin tabbatar da shaidu har ɗari shidda ,na yin amfani da hanyoyin kisan gilla da tsohon shugaban ya riƙa yin amfani da su akan jama'a domin ci gaba da riƙe mulki.Idan kuma har hakan ya tabbata kotun zata tuhume shi da laifukan, kana ya fuskanci shari'a.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi.