Larry Nassar zai yi shekaru 175 a kurkuku | Labarai | DW | 24.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Larry Nassar zai yi shekaru 175 a kurkuku

Wata kotu a Amirka ta yankewa tsohon likitan wasannin motsa jiki na mata, hukuncin daurin rai da rai a kurkuku bisa laifukan cin zarafi da yin lalata da matan da ya yi musu horo a shekarun baya.

Alkalin da ya yanke wa Larry Nassar hukuncin daurin je ka ka mutu Rosemarie Aquilina, ya fadawa Nassar cewa " Na sa hannu kan wa'adin rayuwarka, ina alfahari da yanke maka hukuncin daurin rai da rai saboda ba ka cancanci yin rayuwa a wajen kurkuku ba har abada."

Sai dai kamin yanke wannan hukuncin Nassar mai shekaru 54, ya nemi afuwar 'yan mata matasa da ya ci wa zarafi amma wata daga cikin 'yan matan da ya ci zarafinsu ta ki gafarta masa inda ta fashe da kuka a bainar jama'a a kotu.