Lamura suna kara dagulewa | Labarai | DW | 18.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Lamura suna kara dagulewa

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dubban mutane sun tsere daga gidaje a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane dubu 210 suka tsere daga gidaje, cikin makonni biyu a kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, yayin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula.

Ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius ya bayyana wani shirin kasashen Turai na tura dakaru zuwa kasar, domin magance rikicin da ake samu.

Kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta fada cikin rikicin bayan 'yan tawayen Saleka sun kifar da gwamnatin Shugaba Francois Bozize cikin watan Maris, inda Michel Djotodia ya dauki madafun iko, kuma Musulmai na farko da ya mulki kasar da gabili Kiristoci ne. Kuma yanzu rikicin da ake samu na da nasaba da addini.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh