Lamura a Hong-Kong ba su sauya ba | Labarai | DW | 18.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Lamura a Hong-Kong ba su sauya ba

Masu zanga-zanga a Hong Kong sun ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen cimma burinsu, sai dai bisa dukkan alamu gwamnatin yankin ba za ta ba da kai bori ya hau cikin sauki ba

Gwamnatin Hong-Kong ta ce za ta sake kaddamar da tattaunawa tare da daluban da ke zanga-zanga ranar talata mai zuwa, bayan da aka shafe kwanaki uku 'yan sandan na dauki ba dadi da masu zanga-zangar wadanda suka janyo tsaiko wajen tafiyar da ayyukan yau da kullun a yankin sakamakon yawan zanga-zanga da tattare hanyoyin zirga-zirga.

Shugaban birnin Leung Chung Ying ya sauya ra'ayinsa a wani matakin bazata ranar alhamis, ya sanar da cewa za su koma tattaunawa da kungiyar daluban bayan da suka katse tattaunawar da suka fara mako guda da ya gabata.

Sai dai duk wani fata na samun cigaba kalilan ne, domin bisa bayyanan kamfanin dillancin labaran AFP na Faransa, zai yi wuya gwamnatin ta amince da mahimman bukatunta wadanda suka hada da yin murabus din shugaba yankin Leung Chun-ying da kuma gudanar da zabe mai inganci a shekara ta 2017.