1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lam:Haramta dodon fuskanta a zanga zanga

Abdullahi Tanko Bala
October 4, 2019

Shugabar yankin Hong Kong carrie Lam ta sanar da haramta amfani da dodon fuska a dukkan wata zanga zangar da ba a amince da ita a hukumance ba.  

https://p.dw.com/p/3QkX0
Hongkong Proteste
Hoto: Reuters/A. Perawongmetha

Wannan na kunshe ne a cikin wata sabuwar doka da za ta fara aiki a tsakar daren wannan juma'ar.

Ana sa ran gwamnatin za ta nemi sahalewar majalisar dokoki kan sabuwar dokar.

Duk wanda aka samu ya karya dokar yana iya fuskantar hukuncin daurin shekara daya a gidan yari ko kuma tarar dala 25,000 na Honng Kong kwatankwacin dalar Amirka 3,200

Shugabar yankin Carrie Lam ta ce Hong kong na cikin dokar ta baci sai dai kuma tana fuskantar gagarumin hadari bayan wata mummunar zanga zanga da ta karade birnin. Ta ce dole ne a kawo karshen tarzomar.