1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Matssiya 'yar Ruwanda ta samu lambar yabo

December 22, 2020

Kungiya da ke bayar da kyauta yabo ga matasa masu hazaka da ba su wuce shekaru 18 zuwa 30 ba karrama matashiya Christelle Kwizera 'yar Ruwanda lambar girmamawa.

https://p.dw.com/p/3n4lk
Internationaler Tag des Wassers
Hoto: dapd

Kimanin mutane miliyan dubu biyu ne ke fama da karancin ruwa mai tsafta a daukacin kasashen duniya, Ruwanda na cikin kasashen. Sai dai wata matashiya mai suna Christelle Kwizera ta sadaukar da kanta wajen samawa kimanin mutane dubu 70 ruwa kowace rana.

Kokarin da Christelle Kwizera mai shekaru 27 ke yi na wadata al'ummar Ruwanda da ruwa mai tsafta, ya sanya wata kungiya da ke bayar da kyauta yabo ga matasa masu hazaka da ba su wuce shekaru 18 zuwa 30 ba karrama matashiyar da lambar girmamawa.

Matashiyar kuma Injiniya ta yi amfani da dutse daya wajen jifar tsuntsu biyu inda kokarin ya samawa matasa 'yan uwanta da ayyukan yi. Shirin na samar da ruwan amfanin yau da kullu wanda matasan su ka yi wa lakabi da Water Access Rwanda ya dukufa wajen haka rijiyoyin burtsatse na bore hole a fadin kasar wanda Christelle Kwizera ta ce bukatar hakan ne ya sa su shiga wannan aikin.

Wani al'amari da ya kara baiwa matasan kwarin gwuiwa shi ne hasashen da aka yi na cewa agajin da kasashen Afirka ke samu daga ketare zai ragu sakamakon matsalar tattalin arziki da ake fuskanta a duniya, wanda dama ce ga 'yan Afirka su tashi tsaye in ji Christelle Kwizera.

Divine Muhayimana wata ce da ke kula da wata cibiyar samar da ruwa da shirin na Water Access Rwanda ta samar a unguwar da take da zama ta ce sai godiya.

Duk da cewa masu amfani da ruwan da aka samar na biyan wani abu wanda bai taka kara ya karya ba, matashiyar dai na da kudurin fadada shirin zuwa wasu karin kasashe 12 na Afirka.