1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zubar da jini ba tsayawa illa ne ga halittar bil Adam

Abdourahamane Hassane
August 2, 2019

Jini yakan iya zuba ta sanadin rauni da dan Adam ke iya fuskanta, amma kuma jinin ya tsaya ba tare da saka magani ba. Wasu jama'ar kuma rauni kadan suke samu komi kankantarsa daga nan jini tsinke ya kuma ki tsayawa abin ya kan samu kamar a wajen haifuwa ko yin kaciya ga yara, ko mata dake yin haila.Shirin Lafiya Jari ya duba matsalar da yadda ta ke shafuwar jama'a a wasu kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/3NECU

Eric Adolf von Willebrand shi ne ya tantance wannan cuta ya kuma ganotra. Mata su suka fi kamuwa da wannan ciwo hasalima musamman ma wadanda suka yi fama da zubar jini a wjen haifuwa kuma jinin ya ki tsayawa ko wajen al'ada. 

Halitar dan Adam a tsare take kamar yadda Allah ya tsara abinsa zubar jinin dai na iya zama babbar illa da ta kan iya hadasa krancin jini a cikin jikin dan Adam abinda kan iya kaiwa har zuwa ga rasa rai. Jini yakan iya zuba ta sanadin rauni da dan Adam ke iya fuskanta, amma kuma jinin ya tsaya ba tare da saka magani ba. Wasu jama'ar kuma rauni kadan suke samu komi kankantarsa daga nan jini tsinke ya kuma ki tsayawa abin ya kan samu kamar a wajen haifuwa ko yin kaciya ga yara, ko mata dake yin haila.Shirin Lafiya Jari ya duba matsalar da yadda ta ke shafuwar jama'a a wasu kasashen Afirka.