1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bullar sabbin nau'oi na kututarta a Nijar

Zainab Mohammed Abubakar YB
February 15, 2019

Kididdigar shekara ta 2012 na nuni da cewar Jamhuriyar Nijar na da wadanda ke dauke da cutar kuturta sama da dubu cikin nakasassun da ke cikin fadin kasar da ke zama cikin masu tasowa.

https://p.dw.com/p/3DRQQ
Symbolbild Lepraforschung Jacinto Convit
Hoto: Gregory Pourtier/AFP/Getty Images

Tun daga shekara ta 1873 aka samu bullar cutar kuturta a doron kasa, kama daga wancan lokaci zuwa yanzu gwamnatoci da hukumomin kiwon lafiya sun duka ka'in da na'in wajen yaki da cutar. To sai dai a daidai lokacin da duniya ke samun nasarar kawar da ita, ana cigaba da samun bullar wasu nau'oin cutar a kowace shekara, wanda  al'umma a yawan lokuta ke nuna kyama ga masu dauke da ita. Mal Buzu Suyudi,  jami'in lafiya mai kula da yaki da cutar kuturta da taron fuka a Damagaram, jiha ta biyu da ke fama da wannan cuta ya ce ana samun ci gaba a kokarin kawar da ita.

To sai dai masu fama da wannan lalura sun koka da tarin matsaloli da suke fuskanta musamman yadda ba'a basu kulawa ta musamman kamar yadda Mal Aminu ya nunar. A tattaunawar da wakilimmu Larwana Malam Hami ya yi da shi, Iliya Bawa ya ce lamarin ba mai sauki ba ne a bangarensu.

Lepra in Indien
Masu wannan cuta dai kan fuskanci kyama a cikin al'ummaHoto: AFP/Getty Images

A cewar Mai gari wanda shi ne ke taimakawa wajen kai su asibiti ya shaida wa Larwana cewar kuturta ta rabu kashi biyu.

To sai dai wasu sun yi amanar cewar, wannan cuta ba wata matsala ba ce a yanzu idan aka kwatanta da shekarun baya kamar yadda Halima Garba da ke zama daya daga cikin surikan masu wannan cuta ta nunar.

Wata matsala da wadanda ke fama da larurar kuturta ke fama da ita dai shi ne rashin aikin yi kamar yadda daya daga cikinsu Amina ta shaida wa wakilinmu. Domin jin karin bayani sai a latsa shiri mai alamar dauke da sauti.