1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala wasani kwararru na Turai

Gazali Abdou Tasawa SB
May 23, 2018

Kungiyar Barcelona ta zama zakara tsakanin kungiyoyin kwallon kafa na Spain, haka aka kammala irin wannan gasa a sauran kasashen Turai.

https://p.dw.com/p/2yC6Z
Spanien La Liga FC Barcelona v Real Madrid Ausgleich Bale 2:2
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Fernandez

A birnin Barcelona na Spain kungiyar Barcelona ta gudanar da bikin lashe gasar La Liga ta shekarar bana bayan kammala wasan karshe da kungiyar ta barcelona ta lashe da ci daya da babu a gaban Kungiyar Real Sociedad. 'Yan kallo dubu 80 ne dai suka halarci bikin wanda ya gudana  a jumulce da na karrama Iniesta dan wasan tsakiya na kungiyar ta barcelona wanda a jiya ya bugawa kungiyar wasa na karshe bayan da ya share shekaru 22 yana taka mata leda.

Wannan dai shi ne karo na 25 da kungiyar Barcelona ke lashe gasar ta la Liga inda ta samu maki 93 wato tazarar maki 17 tsakaninta da kishiyarta ta real Madrid wacce ta zamo ta uku da maki 76 a yayin da Atletico ke a matsayin ta biyu da maki 79. Duk kungiyoyi uku da kuma Valancia da ke a matsayi na hudu sun samu tikiti shiga gasar cin kofin zakarun Turai. Kungiyoyin Villareal da ke a matsayi ta biyar da Batis Seville da ke a matsayin ta shida za su wakilcin kasar ta Spain a gasar Europa Lig. Kungiyar Seville da ke a matsayin ta bakwai za ta buga wasan ketara siradin shiga gasar ta Europa Lig. Kungiyoyin Malaga da Las Palmas da Deportivo La korona sun sauka zuwa rukuni na biyu na gasar ta La Liga.

Bildkombi, Bildkombo 3 Starfußballer

A fannin kyautar zura kwallaye dan wasan Barcelona Leonel Messi ne a sahun gaba da kwallaye 34, abokin hamayyarsa na Real Madrid Cristiano Ronaldo na bi masa da kwallaye 26, a yayin da Suares na Barcelona ke a matsayin na uku da kwallaye 25. Kungiyar Barcelona ita ce ta fi kowace kungiya zura kwallo a gasar ta la Liga ta bana da kwallaye 99 a yayin da Atletico Madrid ta fi kowace kungiya iya tsare baya inda aka zura mata kwallae 22 kacal a tsawan kakar shekara ta bana.

Italien Juventus Turrin Jubel
Hoto: picture-alliance/NurPhoto/M. Bottanelli

A Italiya ma an kammala kakar wasannin Seri A na shekarar bana. Kuma Kungiyar Juventus ce ta lashe gasar ta bana da maki 95. Kungiyar Napoli na bi mata da maki 91, AS Roma na matsayi na uku da maki77. Wadannan kungiyoyi uku da kuma Kungiyar Inter Milan da ke a matsayin ta hudu da maki 72 sun samu tikitin shiga gasar cin kofin zakarun Turai kai tsaye. Kungiyar ta Inter Milan wacce shekaru shida kenan rabonta da shiga gasar ta cin kofin zakarun Turai ta samu tikitin nata ne a wannan karo bayan da ta doke kungiyar Lazio ci uku da biyu a wasan da suka buga.

Kungiyoyin Lazio da AC Milan za su buga wasannin Europa Lig kai tsaye a yayin da Altanta Bergame za ta buga wasan ketarar siradi na Play off na shiga gasar ta Europa Lig. Kungiyoyin Crotone da Hellas Verone da Benevento sun sauka zuwa rukuni na biyu na Serie A.

Fußball Juventus Turin - Torhüter Gianluigi Buffon
Hoto: picture-alliance/Sportphoto24/G. Maffia

A dai gasar ta Serie A na Italiya Gianluigi Buffon mai tsaron gida na kungiyar Juventus ya yi ban kwana da kungiyar  wacce ya tsare wa gida a wasannin 656 a tsawon shekaru 17 inda ya lashe gasar Seri A sau tara ya kuma dauki Kofin italiya sau hudu . Shi ma dai ya samu karramawa daga 'yan kallo a wasan karshe da ya buga a ranar ta Asabar a gaban 'yan kallo sama da dubu 40. Dubunnan magoya bayan kungiyar ta Juventus ne dai suka yi ta zubar da hawaye a minti na 63 lokacin da aka dakatar da wasan domin karrama jarumin mai shekaru 40 wanda ya baro fili yana zubar da hawaye a daidai lokacin da magoya baya ke rera sunasa suna bayyana shi a matsayin jarumi.

A Najeriya wata tawagar jami'an hukumar kula da wasannin motsa jiki ta duniya wato IOC ta kai ziyara domin duba shirin da Najeriyar ta yi a matsayinta na kasar da ke jerin kasashen da ke so karbar wasannin shekara ta 2022.