Labarin Wasanni | Zamantakewa | DW | 05.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Labarin Wasanni

Fannonin wasanni da sharhi game da kara yawan kasashe da za su halarci gasar neman cin kofin kwallon kafa na duniya da ake karawa duk bayan shekaru hudu.

A gasar Premier na Ingila da aka kara a karshen mako inda kungiyar Crystal Palace ta bi Chelsea har gida da ci 2 da 1. Yayin da Liverpool ta doke Everton da ci 3 da 1. Kana ManUnited ta tashi babu kare bin damo da kungiyar West Brom. Anata bangaren Leicester ta doke Stoke da ci 2 da nema. Itama Tottenham ta bi Burnley har gida ta lallasata da ci 2 da nema. Har yanzu a gasar na Premier Laegue kungiyar Hull ta doke West Ham da ci 2 da 1. Sannan Arsenal ta tashi ci 2 da 2 da kungiyar kwallon kafa ta Man City.

Kawo yanzu Chlesea ke jagorancin teburin na Premier League da maki 69, yayin da Tottenham ke mara mata baya da maki 62. Liverpool tana matsayui na uku da maki 59. Kana Manchester City ta hudu da maki 58, inda Manchester United take matsayi na biyar da maki 53.

A Gasar Bundesliga da Jamus da aka kara a karshen makon kungiyar kwallon kafa ta Werder Bremen ta bi Freiburg gida ta lallasata da ci 5 da 2. A daya bangaren Leverkusen ta tashi 3 da 3 da kungiyar kwallon kafa ta Wolfsburg. Ita ma Ingolstadt ta yi nasara kan Mainz da ci 2 da 1. Sannan Leipzig ta galabaita Darmstadt da ci 4 da nema.

Har yanzu Bayern Mucih ke jagorancin gasar na Bundesliga da maki 65, inda Leipzig ke mara mata baya da maki 52, Hoffenheim tana matsayi na uku da maki 48.

Hukumar kwallon kafa ta Duniya Fifa, ta fadada yadda zata gudanar da gasar cin kofin  kwallon kafa na Duniya na shekara ta 2026 daga kasashe 32 zuwa 48. Nahiyar Africa, na daya daga cikin Nahiyoyin da zasu fi cin gajiyar wannan sabon tsari.

A karshen wannan makon a gasar Tennis da aka kara a Miami da ke Amirka, shahararren dan wasan Roger Federer daga Switzerland ya samu nasara kan dadadden abokin karawarsa a gasar Rafael Nadal dan kasar Spain, da ci 6 da 3, da 6 da 4. Sai dai Akwai yuwwuar Federer dan shekaru 35 da haihuwa zai huta lokacin gasar da za a yi a Faransa saboda murmurewa daga rashin lafiyar da yake fama.

Ranar 22 ga watan biyar na Mayu ake fara gasar na Tennis na Faransa a birnin Apris, kana za a kammala ranar 11 ga watan Yuni. Yana daya daga cikin manyan wasannin Tennis na duniya da ake karawa duk shekara, inda gwanayen 'yan wasa na duniya za su kece raini tsakanin su.