1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gasar neman shiga gasar buga kwallon kafa ta duniya

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 6, 2021

Ina aka kwana a wasan neman shiga gasar kofin kwallon kafa na duniya da za a fafata a kasar Katara a 2022. An kammala gasar guje guje da tsalle-tsalle ta masu bukata ta musamman ta duniya a birnin Tokyo na kasar Japan

https://p.dw.com/p/3zzY5
Das Spiel zwischen Brasilien und Argentinien in Sao Paolo wurde unterbrochen
Hoto: Andre Penner/AP Photo/picture alliance

Ana ci gaba da fafatawa tsakanin kasashen nahiyoyi, a wasannin neman cancantar zuwa gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da Katar za ta karbi bakunci a badi. A karshen mako an yi wasannin da dama, sai dai wanda ya fi daukar hankali shi ne wasa tsakanin Ajantina da Brazi da aka dakatar kafin kammala shi. Dakatar da wasan dai ya biyo bayan dirar mikiya cikin fili da jami'an ma'aikatar lafiya na kasar Brazil mai masaukin baki suka yi, tare da fitar da wasu 'yan wasan Ajantina uku da suka ce sun ki bin umarnin kebance kansu da aka ba su, sakamakon matakai da ake dauka na dakile annobar corona.

An dai dakatar da wasan a mintuna bakwai da fara shi, inda dukkanin kunigiyoyin babu wanda ya zura kwallo a ragar dan uwansa. Jami'an ma'aikatar lafiyar sun nunar da cewa, kamata ya yi 'yan wasan uku da ke buga kwallo a kungiyoyin wasannin Ingila su killace kansu maimakon shiga wasan. Ma'aikatar lafiya ta Brazil din dai, ta sha alwashin cin tarar 'yan wasan Ajantinan hudu, tare kuma da mayar da su kasarsu sakamakon saba ka'idojin dakile annobar coronavirus na kasar. A yanzu haka dai ana dakon hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta yanke hukunci kan makomar wannan wasa.

Kolumbien Copa America 2001
Hoto: Mauricio Lima/AFP/Getty Images

A sauran wasannin kuwa Amirka da Kanada sun tashi kunnen doki 1-1 Venezuela ta sha kashi a hannun Peru da ci 1-0 Uruguay ta lallasa Boliviya da ci 4-2 yayin da aka tashi wasa canjaras babu ci tsakanin Ecuador da Chile 0-0. Idan muka dawo nan nahiyar Turai kuwa, an tashi wasa a karshen mako tsakanin Sweden da Italiya canjaras babu ci 0-0 yayin da Spain ta lallasa Gogia da ci 4-0. Ita kuwa Armeniya ta kwashi kashinta a hannun Jamus da  ci 6-0 yayin kuma da aka tashi wasa Beljiyam da Jamhuriyar Chek 3-0. Nahiyar Afirka ma dai ba a barta a baya ba, domin kuwa ta bi sahun sauran nahiyoyin duniya wajen ci gaba da wasannin tankade da rairaye na neman tikitin halartar gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya ta 2022 da za a buga a kasar Qatar.

An dai dage wasan da za a fafata na neman cancantar shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya tsakanin Morocco da kasar Guinea. Wannan dai ya faru ne sakamkon juyin mulki da sojoji suka yi a kasar ta Guinea, abin da ya tilastaawa Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya wato FIFA dage wannan wasa da za a gudanar a Conakry fadar gwamnatin kasar ta Guinea a wannan Litinin din. Hukumar ta FIFA ta bayyana cewa, ita da takwarata ta Afirka CAF na sanya idanu kan halin rashin tabbas na siyasa da ake ciki a Guinea a yanzu haka, sai dai ba su bayar da karin bayani kan rana da lokacin da za a buga wasan ba.  

Tokio 2020 | Tennis | Novak Djokovic
Hoto: Seth Wenig/AP Photo/picture alliance

Shararren dan wasan kwallon Tennis Novak Djokovic zai fafata da Jenson Brooksby dan kasar Amirka, a zagaye na hudu na babbar gasar Tennis ta US Open da ke gudana a yanzu haka. Idan dai ba a manta ba, Djokovic ya sha alwashin ci gaba da bayar da mamaki a gasar ta Tennis a bana, biyo bayan nasarorin da ya samu a wannan shekarar da muke ciki. 

A gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta masu bukata ta musamman da aka kammala a Lahadin karshen mako a birnin Tokyo fadar gwamnatin kasar Japan. Chaina ce ta zo ta daya da lambobi 207, Zinare 96 Azurfa 60 da kuma Tagulla 51, sai kuma Birtaniya na biye mata a matsayi na biyu da lambobi 124 Zinare 41 Azurfa 38 da kuma Tgulla 45, kana Amirka a matsayi na uku da lambobi 104 Zinare 37 Azurfa 36 da kuma Tagulla 31.

Japan mai masaukin baki kuwa ta kare a matsayi na 11 da lambobi 51 Zinare 13 Azurfa 15 da kuma Tagulla 23 yayin da Jamus ta karkare a matsayi na 12 da lambobi 43 Zinare 13 Azurfa 12 da kuma Tagulla 18. Ita kuwa Najeriya ta kammala gasar ne a matsayi na 33 da lambobi 10 Zinare hudu Azurfa daya da kuma Tagulla biyar. Daga nahiyar Afirka dai, kasashen Tunusiya da Aljeriya da kuma Moroko sun taka rawar gani, inda suka kammala gasar a matsayi na 28 da 29 da kuma 30.