1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Leipzig ta zama zakaran Jamus

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
May 23, 2022

A karo na takwas cikin tarihinta Manchester City ta zama zakaran kwallon kafar Ingila, yayin da Milan ta samu kambun zakaran Italiya. RB Leipzig kuwa, ta lashe kofin kwallon kafar kasar Jamus a karon farko.

https://p.dw.com/p/4BjMH
Kwallon Kafa | Premier League | Manchester City - Aston Villa
Manchester City, zakaran kwallon kafa ta Premier League karo na takwas a IngilaHoto: Stu Forster/Getty Images

Duk da cewa da kyar ta tsira a hannun Aston Villa a wasan makon 38 kuma na karshe, amma Manchester City ta ci gaba da rike kambun zakaran kwallon kafar Premier a Ingilan. Aston Villa ce dai ta mamaye farkon mintuna 15, inda ta zira kwallaye biyu kafin tawagar Kevin De Bruyne ta rama wa kura aniyarta a cikin mintuna biyar kacal: Godiya ta tabbata ga Ilkay Gundogan da ya farke kwallayen biyu da kuma Rodri. Wannan dai shi ne kambu na takwas da Skyblues ta ci a Ingila, kuma karo na hudu a cikin shekaru biyar. A ta bakin mai horas da 'yan wasan Pep Guardiola wannan sabon kambun gasar Premier, na da muhimmanci sakamakon rashin nasara a gasar zakarun Turai a gaban Real Madrid.

Kwallon Kafa | Premier League | Liverpool
Liverpool na dakon lashe kofin zakarun nahiyar TuraiHoto: Alex Livesey/Getty Images

A daya hannun kuma, Liverpool wacce ita ma ta yi fadi tashi don ganin ta zama zakara, ta samu nasara a kan Wolves Wolverhampton da ci uku da daya, sakamakon kwallayen da Salah da kuma Robertson suka ci a dab da kammala wasan. Amma mai horas da 'yan wasan na Liverpool Jürgen Klopp ya tunatar cewa, kakar ba ta kammala ba a gare su, saboda za ta nemi lashe kofin gasar zakarun Turai karo na biyu tun zuwan mai horaswar dan kasar Jamus. Bayan City da Liverpool, Chelsea da Tottenham ne suka lashe tikitin shiga gasar cin kofin zakarun Turan daga Ingila.

Paris Saint-Germain (PSG) - FC Lorient
Paris Saint-Germain ce zakara a lig din FaransaHoto: Jean Catuffe/DPPI media/picture alliance

A Faransa kuwa, ranar karshe ta gasar Ligue 1 ta kasance lokacin da Marseille ta samu tikitin shiga gasar zakarun Turai. Ita dai Marseille ta doke Strasbourg da ci hudu da nema, tare da yin amfani da sakamakon wasan AS Monaco na cancaras biyu da biyu da Lens wajen kai labari. Yayin da Monaco da ke a matsayi na uku a teburin kwallon Faransa, za ta shiga zagayen tankade da rairaya don samun damar shiga gasar zakarun Turai. Yayin da PSG da ta zama zakara ta kammalla kakar wasan da kafar dama, inda ta doke Metz da ci biyar da nema ciki har da kwallaye biyu da zakakurin dan wasanta Kylian Mbappé ya zira. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Kylian Mbappe Lotin ya sabunta kwantiraginsa da kulob din babban birnin kasar Faransan, har zuwa shekarar 2025.

Italiya | Kwallon Kafa | AC Milan
AC Milan ta lashe kakar wasanni ta bana a ItaliyaHoto: Elisabetta Baracchi/ZUMA Wire/IMAGO

A karshen Italiya kuwa, AC Milan ta zama zakara a karon farko tun 2011. Kungiyar ta Milan ta yankin Lombardie ta lallasa Sassuolp da ciuku da nema tare da lashe kambun Scudetto da maki biyu a gaban abokiyar hamayyarta, wacce ta kasance zakaran bara. Olivier Giroud da Franck Kessié ne dai, suka tsara nasarar da C Milan ta samu. Sauran kungiyoyin da suka cancanci zuwa gasar zakarun Turai daga Italiya sune Napoli da Juventus.

SC Freiburg - RB Leipzig
A karon farko, RB Leipzig ta lashe kofin kwallon kafa na JamusHoto: Matthias Koch/IMAGO

A nan gida Jamus, RB Leipzig ta lashe kofin kwallon kafar kasar bayan da ta samu nasara a wasan karshe a kan Freiburg. Babu shakka 'yan wasan mai horas da 'yan wasa Christian Streich za su dade suna tunawa da wannan nasarar da suka yi, saboda ta buga a inda abokiyar hamayya ke samun goyon baya. Hasali ma Freiburg ta fara bude ragar a minti na 19 na wasa. Sannan bayan da aka dawo hutun rabin lokaci korar Marcel Halstenberg da alkali ya yi, ya kashe gwiwar RB Leipig. Sai dai a lokacin ne Leipzig ta farfado ta hanyar cin kwallo ta hannun Christopher Nkunku. Karin lokacin da aka yi daga bisani bai ba da damar banbance dan duma da kabewa ba lamarin da ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida, inda RB Leipzig ta cilla dukkanin kwallayenta a raga, yayin da Freiburg ta baras da biyu. Saboda haka ne Christian Günter na SC Fribourg, wanda ya samu horo a kungiyar tun yana yaro, ya nuna takaicinsa game da rashin samun nasara. A bangaren Leipzig kuwa, an nuna farin ciki sosai domin wannan shi ne karon farko da ta lashe kofin na Jamus. Ita dai kungiyar ta Leipzig da aka kirkiro a 2009, ta fadi sau da yawa a wasan karshe na Pokal a cikin 'yan shekarun nan, ciki har da kakar wasa ta karshe a gaban Dortmund. Wannan lashe kofi na Jamus da Leipzig ta yi, ya ba ta damar tunkarar Bayern Munich da ke rike da kambun zakara, a gasar cin kofin gwani na gwanaye wato Supercup na Jamus da za a yi a ranar Asabar 30 ga watan Yuli.

Gasar cin Kofin Afirka I 2022 | Guinea-Bissau v Nigeria
Nasarar kungiyar kwallon kafa ta 'yan kasa shekaru 20 ta Najeriya Hoto: Samuel Shivambu/empics/picture alliance

A nahiyar Afirka kuwa, RS Berkane ta lashe gasar cin kofin Confederation Cup a gaban Orlando Pirates. 'Yan wasan Berkhane din Morocco sun yi nasara a kan Orlando Pirates ne a bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan da aka yi wasa ba tare da wani ya ci kwallo ba. Sai dai bayan karin lokaci, Youssef Fahl na RS Berkane ya fara zura kwallo a ragar Orlando, ko da shi ke daga bisani 'yan wasan Afrika ta Kudu sun rama wa kura aniyarta a minti na 117 ta kafar Them-bin-kosi Lorch. Sai dai wannan dan wasan ne ya yi sanadin rafka Orlando Pirates da kasa bayan da ya baras da bugun daga kai sai mai tsaron gida. Wannan kofin nahiyar Afirka dai, shi ne na biyu ga RS Berkane ta lashe baya ga wanda ta lashe a shekarar 2020. Ita kuwa kungiyar kwanlon kafa ta 'yan kasa da shekaru 20 ta Najeriya, ta lashe gasar neman tikitin wakiltar Afirka ta Yamma a gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka a shekara ta 2023 da za ta gudana a kasar Masar. Najeriyar ta samu tikitin nata ne bayan da ta doke kasar Benin a wasan karshe na gasar tankade da rairaya ta rukuni na biyu da ta gudana a babban birnin Jamhuriyar Nijar wato Yamai.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani