AMA
June 3, 2019Talla
Bayan tsawon lokaci ana samun abubuwan ban mamaki da zaman zullumi a bana game da gasar neman cin kofin zakarun nahiyar Turai. A karshen magoya bayan kungiyar Liverpool da ke Ingila sun kwashe tsawon karshe mako suna shagalin lashe kofin zakaru na nahiyar Turai bayan doke kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ita ma daga Ingila, a wasan karshen da ya wakana a birnin Madrid na kasar Spain, inda milyaoyin mutane a sassan duniya suka kallo wasan kai tsaye ta akwatunan talabijin, kuma an tashi wasan biyu da nema: