1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Labarin Wasanni

Suleiman Babayo LMJ
February 22, 2021

Ko kun san yadda ta kaya a karshen mako a wasannin lig-lig na Turai da ma wasu harkokin wasanni a duniya da ma nahiyar Afirka? Ku saurari sakamakon wasannin.

https://p.dw.com/p/3piYu
Fußball Bundesliga | Schalke 04 vs Borussia Dortmund | Tor 0:4 Haaland
Borussia Dortmund na kokarin cire wa kanta kitse a wutaHoto: Martin Meissner/AP Photo/picture alliance

A wasannin lig na Jamus da ake kira Bundesliga, a karshen mako kungiyar kwallon kafa ta Wolfsburg ta lallasa Arminia Bielefeld da ci uku da nema, Freiburg ta sha kashi a hannun Union Berlin da ci daya mai ban haushi. A fafatawar da aka yi kuwa tsakanin Eintracht Frankfurt da Bayern Munich kuwa, Bayern din ta sha kashi da ci biyu da daya a hannun mai masaukin bakinta Frankfurt.

Stuttgart ta lallasa Cologne da ci daya da nema yayin da Schalke 04 da ba ta shiga kakar wasannin ta bana da kafar dama ba ta sha bugun kawo wuka da ci hudu da nema a hannun Dortmund da ita ma a bana take cikin halin kila wa kala. An tashi wasa kunnen doki daya da daya tsakanin Augsburg da Leverkusen, yayin da RB Leipzig ta lallasa  Hertha Berlin da ci uku da nema, ita kuwa Hoffenheim ta samu nasara ne a kan Werder Bremen da ci hudu da nema.

TSG Hoffenheim v SV Werder Bremen - Bundesliga
Fafatawa tsakanin TSG Hoffenheim da SV Werder BremenHoto: Alex Grimm/Getty Images

Tawagar yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist da ke jihar Bauchi a Tarayyar Najeriya ta tsallake rijiya da baya, biyo bayan hadarin da suka samu a hanyarsu ta zuwa wasa da kungiyar Dakada United ta jihar Akwa Ibom, inda motarsu ta kone kurmus yayin da ita ma kungiyar Adama United take cikin wata matsalar sakamakon harin da 'yan garkuwa da mutane suka kai musu har kuma suka yi nasarar awon gaba da direbansu.

Gwamnati Isra'ila ta ce tana fatan yi wa daukacin 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsallenta da za su halarci gasar Olympics a birnin Tokyo na kasar Japan, allurar riga-kafin annobar cutar coronavirus zuwa watan Mayu mai zuwa. Kwamitin kula da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na Olympic din Isara'ilan ne ya tabbatar da hakan, yayin da Isra'ilan ke zama kasa ta farko a duniya da ta fara bude harkokin rayuwa da zuwa wajen wasannin motasa jiki sakamakaon nasarar allurar rigakafin cutar ta coronavirus. Mutanen da suka karbi alluran guda biyu fiye da mako guda, za su iya koma wa harkokin rayuwa. Yanzu haka an yi wa kimanin kaso 50 na 'yan wasan guje-gue da tsalle-tsallen na Isra'ilan allurar riga-kafin cutar ta coronavirus.