1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni 01.08.2022

Mouhamadou Awal Balarabe M. Ahiwa
August 1, 2022

A karon farko cikin tarihi, Ingila ta doke Jamus tare da lashe kofin mata ta Turai. Bayern Munich ta mamaye Leipzig a gasar gwani na gwanayen Super Cup ta Jamus.

https://p.dw.com/p/4EyRA
Women's Euro 2022 - Finale - England vs Deutschland - Pokal
Hoto: Lisi Niesner/REUTERS

Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Ingila ta lashe gasar nahiyar Turai bayan nasarar da ta samu 2-1 a kan Jamus a filin wasa na Wembley a ranar Lahadi 31 ga watan Yuli.  Wannan shi ne karon farko da wata tawagar kwallon kafa ta Ingila ta lashe muhimmin kofi tun bayan gasar cin kofin duniya ta maza a 1966 wato shekaru 56 da suka gabata.

Sai da a kai ga kari lokaci ne 'yan matan Ingila suka zira kwallon karshe a minti 111 da fara wasa, tare da yin turjiya na tsawon mintuna goman karshe don hana takwarorinsu na Jamus rama wa kura aniyarta. Godiya ta tabbata ga Chloe Kelly, 'yar wasan Manchester city da ta ci kwallon na karshe mintuna kalilan banya da ta shigo filin kwallo, amma ta ce hada karfi da karfe da suka yi ne ya sa hakarsu cimma ruwa.

Women's Euro 2022 - Finale - England vs Deutschland Tor (2:1)
Hoto: Michael Regan/Getty Images

A kasar Jamus, kakar wasa ta fara da wasannin farko na neman lashe kofin kwallon kafar Jamus da kuma wasa mai muhimmanci na Supercup wanda Bayern Munich ta samu nasara a kan RB Leipzig.

Da ci 5-3 ne Bayern Munich ta doke Leipzig a ranar Asabar a filin wasa na Red Bull Arena, kuma ta lashe Super Cup na Jamus karo na 10, wato gasar da ke hada kungiyar da ta zama zakara da kuma wacce ta lashe kofin kwallon kafar kasar. Sabon dan wasanta na gaba Sadio Mane ya zura kwallonsa na farko a hukumance, a wasan da 'yan Bayern suka mamaye wasan a farkon rabin lokaci da kwallayen da Jamal Musiala da Sadio Mané da Benjamin Pavard.

A Ingila ma, an kaddamar da kakar wasa inda aka gudanar da wasan da aka fi sani da Community Shield, wanda ke adawa da kungiyar da ta lashe kambun zakara da wacce ta ci kofin FA. Kuma a bana Liverpool ce ta yi nasara da ci 3-1 a kan Manchester city a Leicester. Sai dai Jürgen Klopp da ke horas da Liverpool ya ce wannan wasa ya kasance zakaran gwajin daji na sabuwar kaka a gare su.

A Faransa ma, wasan gwani na gwanayen ya gudana, inda Paris Saint Germain da ke rike da kambun zakara ta lallasa Nantes da ke rike da kofin kasar da ci 4-0, sakamakon kwallaye da Lionel Messi da Neymar da kuma Sergeo Ramos suka ci.

Fußball | Thomas Tuchel |  Paris Saint Germain
Hoto: imago/Sportimage/M. McNulty

A Birmingham na Ingila, an shiga kwana na biyar da wasannin commonwealth da ke hada kasashen da Birtaniya da raina da wadanda ke da alaka da kut-da-kut da ita. Sai dai mutane da yawa sun ji rauni a wani hatsari da ya afki a ranar Lahadi a yayin gasar tseren keke, ciki har da dan wasan Birtaniya Matt Walls. An dakatar da wasan bayan afkuwar hatsarin da ya haddasa raunin 'yan tsere takwas.

Wannan dai shi ne karo na 22 da ake gudanar da Gasar ta Commonwealth, duk da cewa ta canza suna sau biyu tun bayan kafa sheakru 92 da suka gabata. Amma kasancewar wata kasa da Afirka bata taba daukar bakuncin gasar ba, bi ya hana kasashen wannan nahiya irin su Najeriya da kenya da Afirka ta kudu taka rawar gani, imma a fannin gje-guje ne ninkaya da sauransu.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani