1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutum sama da 100 sun mutu a fashewar wasu abubuwa a Beirut

Mahamud Yaya Azare RGB/MNA
August 5, 2020

Zaman makoki na mako guda a Labanan sakamakon mutuwa da jikkatar dubban mutane a tagwayen fashe-fashe masu karfi da suka girgiza birnin Beirut.

https://p.dw.com/p/3gQZ5
Libanon | Gewaltige Explosion in Beirut
Hoto: Getty Images/AFP/STR

An shiga zaman makoki a kasar Labanan bayan mutuwar mutum sama da dari a sakamakon fashe-fashen da aka samu a Beirut babban birnin kasar. A yayin da ake ci gaba da aikin ceto, akwai fargabar alkaluman mamata ya karu a saboda munin lamarin.

Mutum sama da dubu hudu, iftala'in na yammacin ranar Talata ya rutsa da su a kasar da ke fama da matsi mafi muni ga tattalin arzikinta tun bayan da ta kawo karshen yakin basasa na sama da shekaru goma sha biyar.

Fashe-fashen sun auku ne kusa da tashar jirgin ruwa da ke birnin na Beirut tuni kuma aka fara cece kuce kan musabbabin aukuwarsu.

Bahasin farko da mahukuntan na Labanan suka bayar na nuni da cewa, wani rumbun nakiyoyin da aka kwace ne tun shekaru shidda da suka gabata, da ke tashar jiragen ruwan Beirut ya fashe. Fashewa ta biyu ta faru ne a gidan Hariri da ke birnin na Beirut. Kantoman birnin na Beirut, Marwan Abboud, ya siffanta lamarin da wanda ya yi kama da harin kare dangi.