1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin kwantar da hankalin masu bore a Labanan

Mohammad Nasiru Awal ATB
October 21, 2019

Gwamnatin kasar Labanan ta amince da jerin sauye-sauye da nufin kawo karshen zanga-zangar da ta zama ruwan dare a kasar.

https://p.dw.com/p/3Rfax
Libanon Krise | Saad Hariri, Premierminister
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Dalati Nohra Lebanese Official Government Photographer

Bayan jerin zanga-zangar adawa da tabarbarewar tattalin arziki da matsalar cin hanci da rashawa, a wannan Litinin gwamnatin kasar Labanan ta fara daukar matakai da nufin kwantar da hankalin masu bore a kasar. Yanzu haka dai gwamnati ta amince da wani shirin sauyi da kuma kasafin kudin shekarar 2020.

A jawabin da ya yi ta gidan telebijin Firaminista Saad Hariri ya ce buri shi ne a rage yawan gibin kasafin kudin da a yanzu ya kai kashi 7 cikin 100 zuwa kashi 0.6 cikin 100 a shekara mai zuwa.

"Na farko kasafin zai samu gibi na kashi 0.6 bai kuma kunshi sabon haraji ko karin haraji a kan jama'a ba. Na biyu fannonin banki da babban banki za su taimaka wajen rage gibin kasafin da kudi dala miliyan dubu 3.4 wanda ya hada da sabon haraji kan bankuna. Na uku shi ne za a rage albashin shugaban kasa mai ci da tsoffin shugabannin kasa da na ministoci da na wakilan majalisa da kashi 50 cikin 100."

Sai dai masu zanga-zanga da suka yi gangami a birnin Beirut sun yi ta sowa lokacin da Firaministan ke jawabin bayyana wadannan matakan da aka dauka.