1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kyautar allurar rigakafin corona ga kasashe matalauta

Ramatu Garba Baba
May 21, 2021

Manyan kamfanonin hada magunguna sun dauki alkawarin raba wa kasashe matalauta allurar rigakafin corona kimanin biliyan biyu don ganin an dakile annobar daga doron kasa.

https://p.dw.com/p/3tlBf
Symbolbild Corona Impfstoff Biontech und Pfizer
Hoto: Joel Saget/AFP

A wani abu mai kama da a gudu tare don a tsira tare, Kamfanonin hada magunguna na Pfizer da BionTech, sun dauki alkwarin tallafa wa kasashe matalauta da riga-kafin annobar corona kimanin biliyan biyu, za a kasafta riga-kafin kashi biyu, inda za a soma raba kaso na farko a wannan shekarar, kaso na biyun a shekara mai zuwa a nahiyoyin Afirka da Asiya.

Sanarwar na zuwa ne, bayan da wani rahoto na mujallara Lancet, ya nunar da cewa, 'yan asalin nahiyar Afirka sun fi shiga hadarin mutuwa daga cutar mai kama numfashi a sakamakon rashin wasu muhinmman kayayyakin aiki da asibitoci ke bukata don ceto mara lafiya daga mutuwa.