Kyautar bajinta ta majalisar Turai | Siyasa | DW | 22.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kyautar bajinta ta majalisar Turai

Wani likitan mata,ɗan Jamhuriyar Demokaraɗiyyar Kwango ya samu kyautar bajinta da Turai ke bayarwa duk shekara, bisa aiyyukan agaji da ya yi.

Likitan Denis Mukwege wanda darekta ne a asibitin ƙwararru da ke a gabashin Kwango, ya samu wannan kyautar ne bisa yadda yake bai wa mata da ake cin zarafinsu tallafi. Ya dai yi fice bisa adawa da cin zarafin mata musamman a yankin ƙasar da ke fama da tashin hankali, inda ake samu matuƙar yi wa mata fyade. Therese Mema na cikin ƙungiyoyi da ke aiki a yakin na gabashin Kwango kuma ta faɗi irin shaidar da suka yi wa likitan da aka bai wa kyautar.

"Yana kasance wa da matan a ko wane lokaci,yana ba su shawara kan halin da suke ciki. Wannan shi ya sa muke alfahari da cewar duk duniya ta shaida bisa aikin da ya yi kuma aka ba shi wannan kyautar."

Ƙoƙarin da likitan ya yi shi ya sa,ya samu wannan kyauta

Shi dai wannan likitan ya taɓa samun kyautar bajinta ta Olof Palme, inda a wacan lokaci ya shaida wa DW cewar wannan aikin da yake ya samo asali bisa horon da mahaifinsa wanda Pastor ne ya ba shi. Don haka tun bayan kammala karatun likita a ƙasar Burundi ya koma ƙasarsa ta haifuwa domin tallafa wa marafa galihu.

"Ma haifina wanda Pasto ne, ya bani horon kula da muta ne, A gare ni wannan ƙaramin abu ne. Amma sai na faɗawa kai na yana da kyau na ci gaba da ba da wannan taimako."

Ƙungiyoyin agaji na ƙasashen ƙetare na yabawa da wannan kyauta

Su ma dai ƙungiyoyin agaji daga ƙetare da suke aiki tare da Mukwege a ƙasar Kwango sun yaba da wannan kyautar da majalisar dokokin tarayyar Tuirai ta ba shi. Misali Gisela Schneider darakta a ƙungiyar agaji ta likitocin Jamus ba ta ɓoye munarta ba ga wannan kyauta ba.

"Wannan mataki mai kyau ne.Domin shi mutum ne mai karamci. wanda ya ba da himma wajen zaman lafiya da adalci, musamman a gabashi Kwango da kuma daukacin rayuwarsa"

Tun a shekara ta 1988 Majalisar dokokin Tarayyar Turai ke ba da wannan kyauata da ka sani kyautar Sachrow, inda ake ba da kyautar ga mutanen da suka yi wani abu na musamman bisa adawa da cin zarafin lokutan yaƙi, da kuma waɗanda suka yi fautikar adawa da tsatsauran ra'ayi.

Wannan likita ɗan ƙasar Kwango Denis Mukwege za a ba shi kudi har Euro dubu 50,000 a wannan kyautar da ya samu, bisa agazawa matan da ake yi wa fyade a ƙasarsa ta haifuwa.

Sauti da bidiyo akan labarin