Kwango za ta yi wa dokar ma′adanai kwaskwarima | Labarai | DW | 11.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwango za ta yi wa dokar ma'adanai kwaskwarima

Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango ta sanar da shirin yi wa kundin tsarin aikin hakar ma'adanai na kasar gyaran huska ta yadda kasar za ta fi cin moriyar arzikin karkashin kasar da Allah ya huwace mata

Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango ta sanar da shirin yi wa kundin tsarin aikin hakar ma'adanai na kasar gyaran huska ta yadda kasar za ta fi cin moriyar arzikin karkashin kasar da Allah ya huwace mata, musamman ma'adanin Cobalt da na jan karfe wadanda farashinsu ya yi tashin gobran zabo a yau a saman kasuwannin duniya. 

Mahukuntan kasar Kwangon dai sun bayyana cewa kamfanonin kasashen waje da ke aikin hakar arzikin ma'adanai a kasar na ci da gumin kasar a karkashin dokar da ke aiki a yanzu. 

Wannan mataki da hukumomin Kwangon ke shirin dauka na zuwa ne a daidai loakcin da a kasuwannin duniya farashin ma'adanin Cobalt wanda ake kera batiran salula da na motoci da shi ya yi tashin gobran zabo inda ake sayar da ton guda dalar Amirka dubu 75, a yayin da na jan karfe ya kai dalar Amirka dubu 70 wanda ke zama farashi mafi girma a cikin kusan shekaru hudu na baya bayan nan.