1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan tawayen AFD sun hallaka mutane 20 a Kwango

April 8, 2023

A Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango sama da mutane 20 sun bakunci lahira bayan wani hari da ake kyautata zaton masu kaifin kishin addini na kungiyar 'yan tawaye ta ADF ne suka kai.

https://p.dw.com/p/4PqMZ
DR Kongo Kindersoldaten
Hoto: Zanem Nety Zaidi/DW

Shaidun gani da ido sun ce an kai harin ne da maraican Juma'a 08.04.2023 a kusa da wani kauye da ake kira Enebula. Wani dan farar hula da ke yankin ya shaidawa manema labarai cewa kungiyar Allied Democratic Forces mai biyyaya ga kungiyar IS mai da'awar kafa daular Musulunci ta yi wa wasu monoma ne kwantan bauna yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa gida kuma nan take yanke sai da ya kirga gawarwaki 21.

Ko baya ga harin na jiya, a ranar Alhamis da ta gabata ma dakarun wanzan da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun dora wa kungiyar ta AFD alhakin kisan mutane sama da talatin a ranakun biyu da uku ga wannan wata na Aprilu baya ga kuma kisan wasu mutane sama da 60 a watan Maris din da ya shude. 

Kungiyar 'yan tawaye ta AFD ta yi mubayi'a ne ga reshen kungiyar IS da ke tsakkiyar Afirka a shekarar 2019, kuma ko da a watan Maris din da ya gabata Amurka ta saka miliyan biyar na dala ga duk wanda ya ba ta labarin shugaban reshen kungiyar dan asalin kasar Yuganda mai suna Musa Baluku.